Masana a Afirka ta Kudu na gargadin bullar wani sabon nau'in cutar korona

Yadda kwayar cutar korona take

Asalin hoton, Getty Images

Masana kimiyya a Afirka ta Kudu sun yi gargaɗin cewa a na iya samun ɓullar wani sabon nau'in cutar korona daga mutanen da wasu cutuka kamar ƙwayar cutar HIV suka kassara wa garkuwar jiki.

Masanan sun ce akwai wajabcin ƙarin taimako don tabbatar da ganin an yi wa mutanen da suka fi zama cikin hatsari allurar riga-kafi a faɗin duniya.

Akwai abubuwa masu yawa da ke iya raunata garkuwar jiki kamar ciwon suga, da ƙarancin abinci mai gina jiki da kuma wasu hanyoyin magance cutar kansa ko daji.

Ma'aikaciyar agaji Asiphe Ntshongontshi

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Ma'aikaciyar agaji Asiphe Ntshongontshi ta ce har yanzu ana nuna kyama ga masu dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki

Sai dai a Afirka ta Kudu, ƙasar da ta fi fama da annobar cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV, masanan kimiyya a yanzu na nuna damuwa a kan mutanen da ba sa shan magungunan kashe kaifin ƙwayar cutar HIV daidai, waɗanda kuma sanadin haka suka kwanta ciwo, sannan suka kamu da ƙwayar cutar korona.

Garin Masiphumelele, da ke kudu da birnin Cape Town

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Kashi daya bisa hudu na mazauna garin Masiphumelele, da ke kudu da birnin Cape Town, suna dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki

Akwai shaidar da ke nuna cewa ƙwayar cutar korona tana laɓewa tsawon watanni a cikin jikinsu inda take shafe lokacin tana rikiɗa.

Masana kimiyyar sun buga misali da nau'o'in cutar korona da suka ɓulla zuwa yanzu a duniya. Wannan a cewarsu, ba matsala ce da ta keɓanta ga Afirka ta Kudu ba.

Sun yi gargaɗin cewa annobar korona ta kassara yaƙin da duniya ke yi da cuta mai karya garkuwar jiki, lamarin da ya janyo kwantar da ƙarin mutane a asibiti.

Mafita a cewar ƙwararrun a nan ita ce a haɓaka riga-kafin da ƙasashen Afirka ke yi, kuma a gano tare da tallafawa duk mutanen da garkuwar jikinsu ta yi rauni, don ba su ƙarin taimakon da za su iya tabbatar da ganin cikin sauri sun shawo kan duk wata sabuwar yaɗuwar korona da za a iya samu.