WHO: Riga-kafi zai iya aiki kan sabon nau'in Omicron

.

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta tabbatar da cewa riga-kafin da ake da su a halin yanzu na annobar korona za su iya kare waɗanda suka kamu da nau'in Omicron.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwajin farko da aka yi kan sabon nau'in a Afrika Ta Kudu ke nuna cewa akwai yiwuwar riga-kafin Pfizer zai iya yaƙar sabon nau'in.

Masu bincike sun bayyana cewa an samu raguwa matuƙa kan yanayin yadda riga-kafin ke daƙile sabon nau'in.

Sai dai Dakta Mike Ryan daga Hukumar Lafiya Ta Duniya ya bayyana cewa babu wata alama da ke nuna cewa Omicron za ta ƙi jin riga-kafi.

"Muna da riga-kafi masu ƙarfi da aka tabbatar suna bayar da kariya daga duka nau'ukan korona a halin yanzu, musamman kan batun tsananin cutar da har za ta kai ga kwantar da mutum, kuma babu wata hujja da ke nuna cewa riga-kafin ba za su bayar da kariya ga Omicron ba," in ji Dakta Ryan, daraktan ayyukan gaggawa na WHO kamar yadda ya shaida wa AFP.

Ya ce bayanan da aka samu a baya sun nuna cewa nau'in Omicron na sa mutane rashin lafiya matuƙa fiye da nau'in Delta da sauran nau'ukan.

Wani sabon bincike da aka yi a Afrika Ta Kudu wanda ba a tantance shi ba, ya gano cewa riga-kafin Pfizer/BioNTech na da ƙarancin ƙarfin yaƙar Omicron sau kusan 40 idan aka kwatanta da sauran nau'ukan.

Sai dai batun a ce Omicron ba za ta ji riga-kafi ba babu tabbas, in ji Farfesa Alex Sigal, wanda wani ƙwararre ne kan cutuka a cibiyar bincike kan lafiya ta Afrika wanda ya jagoranci binciken.

Ya bayyana cewa sakamakon wanda aka samu daga gwajin jini na mutum 12 sun nuna cewa sun samu sauƙi fiye da yadda ake zato.

Farfesa Sigal ya bayana cewa idan aka kwatanta da kamuwa da cutar a baya, akwai yiwuwar riga-kafin za iya bayar da kariya daga sabon nau'in. Wannan na nufin yin riga-kafi sau uku zai iya yin amfani

Masana kimiyya na ganin cewa kamuwa da cutar a baya, da kuma yin riga-kafi har sau uku, akwai yiwuwar a samu ƙaruwa a matakin yaƙi da cutar haka kuma zai iya kawo kariya don kada cutar ta yi ƙamari.

Ana sa ran nan da kwanaki masu zuwa za a fitar da ƙarin bayani kan yada Pfizer ke aiki kan Omicron.

Babu wata hujja mai ƙarfi da ke nuna yadda Moderna da Johnson & Johnson da kuma sauran riga-kafin za su iya bayar da kariya daga sabon nau'in.

..

Asalin hoton, Getty Images

Omicron ne nau'i na korona da a halin yanzu aka tabbatar ya fi ko wane sauyawa.

An soma gano nau'in ne a Afrika Ta Kudu, inda a yanzu ake samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar sosai.

Mai magana da yawun Firaiministan Birtaniya Boris Johnson, ya bayyana cewa alamomin cutar na farko-farko sun nuna cewa Omicron zai fi saurin bazuwa a tsakanin mutane fiye da nau'in Delta.

Sai dai babu wani tabbaci da ke nuna cewa nau'in Omicron na da tsanani fiye da sauran.

An tabbatar da cewa sama da mutu miliyan 267 sun kamu da korona a duniya inda kuma sama da mutum miliyan biyar suka mutu tun bayan da cutar ta ɓulla a 2020.

2px presentational grey line