Omicron: Shin ba a yi wa Najeriya adalci ba wajen hana 'yan kasarta shiga Birtaniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Jake Horton
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
Gwamnatin Birtaniya ta sanya 'yan Najeriya cikin 'yan kasashen da ta hana shiga kasarta, wani mataki da gwamnati ta ce ta dauka ne domin yaki da sabon nau'in cutar korona na Omicron mai saurin yaduwa.
Ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya, ya mayar da martani da cewa matakin nuna wariyar launin fata ne.
Shin me ya sa aka sanya Najeriya cikin kasashen, kuma an yi mata adalci kuwa?
Wadanne ne kasashen da aka hana shiga Birtaniya?
Najeriya dai ita ce kasar Afirka ta baya-bayan nan da Birtaniyar ta sanya cikin kasashen, sauran sun hada da Afirka ta Kudu, Namibia, Zimbabwe, Botswana, Lesotho, Eswatini, Angola, Mozambique, Malawi da kuma Zambia.
Mutanen da aka amince su shiga Birtaniya daga wadannan kasashen dai su ne 'yan asalin Birtaniya, ko mazauna kasar ko kuma 'yan arewacin Ireland.
Wadanda suka shigo daga wadannan kasashen za a bukaci su killace kansu a otal, kuma su za su kula da kansu tsawon kwanaki 10.
An sanya kasashen cikin wadanda ba amince su shiga Birtaniya ba saboda sabon nau'in Omicron da aka fara ganowa a Kudancin Afirka.
Sai dai ganin cewa dukkan kasashen na nahiyar Afirka ne wasu ke zargin cewa babu adalci cikin lamarin kuma tsabar mugunta ce.
Wadanne matakai ake bi domin sanya kasa cikin masu hadari?
Matakin sanya kasa a irin wannan nayi dai ya danganta da hadarin da binciken kwararru daga Cibiyar Biosecurity Centre (JBC) ya gano, wadanda suka hada da:
- Ingancin wurin bincike, ciki har da bincike kan nau'in cutar
- Adadin wadanda aka gano sun kamu da cutar
- Sanin ko mutane sun kamu da cutar a inda suke, ko wasu ne suka shigo da cutar daga wata kasar
- Sanin ko an shiga wata kasa da sabon nau'in cutar, ciki har da Birtaniya
- Ingancin tafiye-tafiyen masu alaka da Birtaniya
Me ya sa aka sanya Najeriya cikin kasashen?
Gwamnatin Birtaniya ta ce an sanya Najeriyaa cikin jerin kasashen da ke da hadari ne saboda:
- Kwakkwaran bincike ya gano akwai nau'in Omicron a Najeriya
- Yawancin wadanda aka gano sun kamu da cutar a Birtaniya, akwai alakar sun yi balaguro zuwa Najeriya
- Najeriya na daga alakar kut-da-kut da Afirka ta Kudu, inda aka fara gano nau'in na Omicron

Asalin hoton, Getty Images
JBC ya gabatar da rahoto da takaitacciyar kididdiga domin shaida wa kasashen da aka hana shiga Birtaniyar, amma kawo yanzu ba aike ko wallafa ta Najeriya ba.
Matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na kara Najeriya cikin kasashen, ta ce yawancin wadanda aka samu da Omicron da aka samu a kasar suna da "alakar balaguro daga Najeriya da Afirka ta Kudu."
Mutum nawa ne suka kamu da Omicron a Najeriya?
Cikin makon da ya gabata an samu masu Omicron 90, amma wadanda suka kamu da ita a Najeriya ba su taka-kara-sun-karya ba, idan aka kwatanta da kasashen Turai - sai dai ba a cika yin gwaji a kasashen Afirka ba kamar yadda ake yi a Turai.
A makon karshe na watan Nuwamba, Najeriya ta kammala gwajin kasa da kashi daya na 'yan kasar, ma'ana yi wa mutum 1,000 gwaji a kowacce rana, idan aka kwatanta da kashi 14 cikin 14 a Birtaniya da kashi 8 a Faransa.
Amma daga karshen watan Nuwambar zuwa 2 ga watan Disamba, Najeriya ba ta samu masu sabon nau'in koronar a gwajin da ta ke yi a kowacce arana idan aka kwatanta da Afirka ta kudu da kasashen turai ba.
Har wa yau, baya ga bambancin tsarin yin gwaji, kasashe na da kididdiga da yadda suke tattara bayanai daban-daban, abin da ke sanya wanda ka yi daga kasashen waje mai sarkakiya.
Gwamnatin Birtaniya na tattara bayanan mutanen da suka yi gwajin korona lokacin da suka shiga kasar.
Na baya-bayan nan shi ne na watan Nuwamba, ya nuna kashi daya na wadanda suka shiga kasar daga Najeriya ne kadai gwaji ya nuna suna dauke da cutar, idan aka kwatanta da wadanda suka shiga daga wasu kasashen turai, a iya cewa adadin dan kalilan ne.

Yaya batun masu nau'in Omicron?
Cibiyar binciken cutuka masu yaduwa ta Najeriya(NCDC) ta gano mutum 3 mau sabon nau'in korona na Omicron a kasar, duka suna da alaka da balaguro Afirka ta Kudu.
Wannan kalilan ne a kan na kasashen turai ciki har da Birtaniya, wadda ta gano mutum 336 dauke da sabon nau'in.
Sai dai kididdigar NCDC ta kwanaki biyar ta suka gabata na nuna adadin ka iya fin hakan.
Hanyoyin da ake yi ba wajen gano cutar sun yi karanci a Najeriya, idan aka kwatanta da Birtaniya ko Afirka ta Kudu, misali, yanayin yadda Omicron ke yaduwa ta yiwu ta jima da fara wadari.
A Ingila kadai an samu mutum 21 masu Omicron, da suka yi balaguro zuwa Najeriya kamar yadda Sakataren Lafiyar Birtaniya Sajid Javid ya bayyana.
Yaya batun yawan wadanda aka yi wa Rigakafi?
Ana kuma duba yawan mutanen da kasa ta yi wa allurar rigakafin cutar duk da cewa wannan dai "ba cikakkiyar hujja ba ce" na yaduwar cutar.
Yawan wadanda aka yi wa rigakafi a nahiyar Afirka bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da wasu kasashen duniya.
Ranar 5 ga watan Disamba, Najeriya ta yi wa kashi 4 da digo 8 na rigakafin da aka yi wa mutum 100 amfani da ita, yayin da sama da kashi 178 aka yi wa mutum 100 ita a Birtaniya.










