Har yau 'yan bindiga na karbar haraji daga manoman Birnin Gwari

Rahotanni daga Birnin Gwari da wasu sassan jihar Kaduna sun ce `yan fashin daji na ci gaba da tafka aika-aika, bayan matakin buɗe layukan waya a jihar.
Wasu mutanen yankin sun ce 'yan bindigan sun hana manoma kwashe amfanin gona, duk da hare-haren da jami'an tsaro ke kai wa maharan.
Alhaji Zubairu Idris Abdurra'uf shi ne Ɗan Masanin Birnin Gwari, ga kuma ya yi wa BBC karin bayanikan halin da yankin Birnin Gwari ke ciki.
"Sake bude layukan sadarwa da aka yi ya ba al'umomin Birnbin Gwari damar tuntubar 'yan uwansu da kuma sanar da jam'ian tsaro halin da suke ciki da zarar 'yan bindiga sun kai mu su hari."
Sai dai ya ce babu abin da sauya a bangaren rashin tsaro.
"Halin da ake ciki shi ne tamkar jiya-i-yau, domin har yanzu yan bindiga na kai hari kuma duk da cewa jami'an tsaro na kai mu su farmaki, har yau din nan ba a daina kai hare-haren ba.".
Ya kuma ce abin takaici ne har wannan lokaci a ce barayin dajin na saka wa manoman yankin harajin amfanin gonakinsu.
"Manoma da dama za su yi asarar amfanin gona saboda 'yan bindiga sun hana su shiga gonakin sai bayan sun biya su haraji domin su yi girbin abin da su ka shuka."
A baya baya nan rahotanni sun ce rundunar sojin saman Najeriyar ta yi nasarar tarwatsa wani gungun 'ya fashin daji da ke addabar matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda aka kashe fiye da mutum 45, ciki har da jagoransu mai suna Ali Kwaja.











