Omicron: Birtaniya za ta hana jirage daga Najeriya shiga kasarta saboda sabon nau'in korona

Filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos, Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Birtaniya za ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ta ware domin daukar karin matakai a kan 'yan kasashensu wajen shiga Birtaniyar, saboda mutane 21 da aka samu dauke da sabon nau'in cutar korona omicron a Ingila, wadanda suka je can daga Najeriyar.

Matakin ya kunshi hana 'yan Najeriyar da ma sauran mutane daga kasar wadanda ba su da fasfo na Birtaniya ko izinin zama a can zuwa.

Wata sanarwa da hukumomin Birtaniyar suka fitar ta ce daga karfe hudu na asuba agogon kasar wato biyar na asubar kenan agogon Najeriya, gobe Litinin 6 ga Disamba matakin zai fara aiki.

Matakin na nufin 'yan Najeriya ko mutanen da suka fito daga kasar wadanda suka kai kwana goma wadanda ba su da fasfo na Birtaniya ko takardar izinin zama a kasar daga ranar ba za su je ba, har sai abin da hali ya yi.

Hakan ya kuma shafi hatta wadanda aka yi wa cikakken rigakafin korona.

Su kuwa wadanda suke da damar shiga kasar daga Najeriyar, wato wadanda suke da fasfo na Birtaniyar da kuma na Ireland tare da masu izinin zama, dole ne su killace kansu tsawon kwana goma a wani wuri da gwamnati ta amince da shi, da zarar sun shiga Birtaniyar.

Matafiya a filin jirgin saman Najeriya

Asalin hoton, Others

Sannan kuma dole ya kasance masu shigar sun gabatar da shedar gwajin cutar koronar guda biyu da aka yi musu da duk biyun suka nuna ba sa dauke da cutar, yayin da ake ci gaba da daukar karin matakan dakile sabon nau'in cutar, Omicron.

Sai dai kuma wannan mataki kamar yadda sanarwar ta nuna bai shafi matafiya da suka yada zango domin sauyin jirgi a Najeriyar ba, wadanda a dalilin sauyin jirgin ne kawai aka bi da su ta can.

Haka kuma matafiya daga Najeriyar har yanzu suna da damar bi ta filayen jirgin saman Ingila, su sauya jirgi zuwa wata kasar da za su je, idan dai suna da takardar izinin bi ta Birtaniyar.

Da take bayani a kan matakin, jakadiyar Birtaniya a Najeriya Catriona Laing ta ce, matakin na wucin-gadi ne domin kare karuwar mutanen da ke dauke da sabon nau'in cutar korona shiga Birtaniya.

Kuma za a sake nazarin matakin bayan sati uku, wato ranar 20 ga watan Disamba kenan.

Jakadiya Laing ta ce ta san cewa wannan mataki zai shafi mutane a kasashen biyu sosai, musamman ma a wannan lokaci na shekara, to amma abu ne da aka yi na kan-da-garki domin kare lafiyar jama'a a Birtaniya, yayin da ake kokarin fahimtar yadda sabon nau'in cutar yake.

Ta ce suna ci gaba da aiki kut da kut da hukumomin Najeriya wajen yaki da annobar, kuma suna yabawa da aikin da Najeriyar ke yi.

Ana yi wa Firaministan Birtaniya Boris Johnson allurar rigakafin korona

Asalin hoton, BORIS JOHNSON/TWITTER

A yanzu dai yawancin mutanen da aka samu na dauke da sabon nau'in cutar koronar a Birtaniya suna da alaka da matafiya daga Afrika ta Kudu da Najeriya.

Kuma a makon da ya gabata mutane 21 da aka bayar da rahoton an samu dauke da cutar daga Najeriya suke.

Ministan lafiya na Birtaniya Sajid Javid ya gaya wa BBC cewa, ''A 'yan kwanakin nan mun samu mutane masu yawa masu cutar wadanda ake alakantawa da zuwa daga Najeriya.''

Ya kara da cewa, ''tuni akwai mutane 27 a Ingila kuma suna karuwa, sannan kuma Najeriya yanzu ita ce ta biyu bayan Afrika ta Kudu a wadanda ke dauke da sabon nau'in cutar ta korona, Omicron.''

Ministan ya ce gwamnati ta tsaya tana nazari ne tun bayan bullar sabon nau'in cutar koronar ta san irin matakan kariya da ya kamata ta dauka.

Ya ce abu ne da yake a fili daman wanda kuma gwamnati ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan har ya zama dole.

Gwamnatin Birtaniyar ta dauki matakin ne bayan matsin lamba da take ta sha a makon.