Abubakar Malami: 'Barazanar 'yan bindiga ta sa muka ayyana su da 'yan ta'adda'

Ministan shari'a a Najeriya, Abubakar Malami, ya tabbatar da matakin da gwamnati ta dauka na ayyana 'yan bindiga da suke addabar kasar musamman yankin arewa maso yamma da 'yan ta'adda.

Malami ya bayyana hakan ne a wani shiri na gidan talabijin din Channels da ya shafi siyasa a ranar Laraba 1 ga watan Disamba.

Malamin ya ce "idan ana maganar tsaro da halin da Najeriya ke ciki da irin barazanar da 'yan bindigar ke yi wa ƴan ƙasa ta hanyar sace mutane domin neman kuɗin fansa, da kawo rashin zaman lafiya, da satar dabbobi, za mu ga cewa babbar matsala ce.

"Idan aka yi duba da yadda aka fara da batun Boko Haram, mun yi ƙokarin ayyana su a matsayin ƴan ta'adda la'akari da irin abubuwan da suke yi da kalubalen da suke jawo wa Najeriya,'' in ji Malami.

Malamin ya ce an tuntuɓi duk masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro kafin ɗaukar matakin, za kuma a hukunta 'yan bindigar ƙarkashin dokokin shari'a na kasar.

Ya ƙara da cewa: ''Muna ci gaba da aiki domin tabbatar da hakan a rubuce, nan ba da jimawa ba za mu sanar da hakan. A ƙarƙashin doka duk wanda ya sace mutane ta hanyar amfani da ƙarfi, ko makamai to ɗan ta'adda ne, kuma kotu za ta hukunta ka ƙarƙashin dokar da ta dace da laifinka,'' in ji Malami.

A makon da ya gabata ne, babbar kotu a Najeriya ta ayyana ƴan bindigar da ke addabar arewa maso gabashin Najeriya da wasu yankunan kasar da matsayin 'yan ta'adda.

Dakta Umar Gwandu shi ne mai taimaka wa ministan a kan harkokin yada labarai kuma ya bayyana cewa wannan matakin da aka ɗauka zai bayar da dama ga jami'an tsaro da masu gurfanarwa a gaban kotu su yi mu'amala da su a matsayin ƴan ta'adda.

Ya ce a yanzu bayan wannan matakin na kotu, ba za a samu wani cikas ba tsakanin al'umma da sauran masu ruwa da tsaki ba idan aka je kai musu farmaki.

Tuni dai wasu ƴan Najeriyar ke muhawara a kan ayyana ƴan bindiga ko masu satar mutanen a matsayin ƴan ta`adda, inda wasu ke ganin cewa ba sai an kai ga tsayawa ana wata ayyanawa ba, idan aka yi la`akari da aika-aikar da suke yi, yayin da wasu kuma ke cewa yin hakan kuskure ne, saboda watakila zai ƙara taurara zukatansu, tare da ta`azzarabarnar da suke yi.

Dangane da haka BBC ta tuntuɓi wani mai sharhi kan harkokin shari'a Barrister Sa`idu Tudun Wada, wanda ƙwararren lauya ne a Kano, inda ya ce ayyana ƴan bindigan a matsayin ƴan ta'addda ba ƙaramar nasara ce ba ga ƴan Najeriya.

"A hukumance, kotu ta samu damar da za ta ayyana duk wanda ta samu da laifin aikata haka ta yanke masa hukuncin kisa, wannan zai tsoratar da su masu aikata laifin.

"Bugu da ƙari shi kansa laifin yanzu da masu aikata shi an faɗaɗa shi, ta hanyar cewa duk wani wanda yake mu'amala ta kusa ko ta nesa ko kuma yake taimaka musu ta hanyar kuɗi, ko karɓar kuɗin ko ɓoye kuɗin, shi ma hukuncin kisa ya hau kansa," in ji Barrister Tudun Wada.

Ya kuma ce a halin gwamnati za ta samu dama wajen tuntuɓar al'ummar duniya wajen neman taimako da kuma haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kawar da wannan matsalar da ta addabi ƙasar.

Matsalar harin ƴan bindiga da satar mutane a Najeriya na neman zame wa al`umma da mahukunta alaƙaƙai, sakamakon ƙunci da asarar rayuka da dukiya da lamarin ke haddasawa. Mahara sun tilasta wa mazauna yankunan karkara ƙaurar dole, suna kona musu gidaje, da hana su noma da sauran sana`o`i.

Tun ana kukan yawaitar satar mutanen a ƙauyuka da biranen wasu jihohi, yanzu mazauna Abuja, babban birnin tarayyar ma, musamman na gefen gari a cikin zullumi suke, duk kuwa da cewa mahukunta na alwashin daukar matakan kariya.