Tanzania: Mutum bakwai sun mutu bayan cin naman kunkuru mai guba

Green sea turtle, Zanzibar Island

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba a san ainihin abin da ke jawo guba a jikin kunkuru ba
    • Marubuci, Daga Maryam Abdalla
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili, Nairobi

Mutum bakwai da suka haɗa da yaro ɗan shekara uku da rabi ne suka mutu bayan cin naman kunkuru mai guba a yankin Tsibirin Pemba a Tanzaniya.

Sannan mutum uku daban kuma suna asibiti ana duba su.

An saba da amfani naman kunkuru a wannan yankin da ke bakin gaɓar teku, amma a yanzu hukumomi sun haramta cin naman kunkuru a yankin.

A wasu lokutan a kan samu naman kunkuru mai gubar chelonitoxism.

Ba a san ainihin abin da ke jawo guba a jikin kunkuru ba amma ana tsammanin yana da alaƙa ne da wani ganye da shi kunkurun ke ci, a cewar cibiyar kula da kunkuru.

A ƙalla iyalai biyar ne suka ci naman kunkurun a yankin da ke tsibiran da ke da ƙwarya-ƙwaryar cin gashin kansu a Zanzibar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, kamar yadda wani jami'in ƴan sandan yankin Juma Said Hamis ya shaida wa BBC.

An fara ganin illar cin naman ne bayan da washe gari yaron ɗan shekara uku da rabi ya mutu da safe, sai kuma wasu biyun suka mutu da daddare yayin da huɗu suka mutu ranar Lahadi.

An kwantar da wasu mutum 38 a asibiti, amma an sallami mafi yawansu sai kuma sauran ukun da suke asibitin a yanzu sun farfaɗo suna samun sauƙi.

A wani saƙo da ya wallafa a Tuwita, shugaban ƙasar Zanzibar Hussein Mwinyi ya aika saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan da abin ya shafa.

Gubar za ta iya yin mummunan tasiri a kan yara fiye da manya, duk da cewa yana iya yi wa manyan ma masu cikakkiyar lafiya illa, in ji cewar cibiyar kula da kunkuru.

A watan Maris ma a Madagascar, mutum 19 da suka haɗa da yara tara ne suka mutu bayan cin naman kunkuru, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sannan an samu irin wannan matsala a yankunan da ke gaɓar Tekun Atalantika a ƙasashen Indonesiya da Micronesiya da Indiya.

Map
1px transparent line