An samu haɗarin 'yan ci-rani mafi muni a mashigar tekun Ingila

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Faransa na ganawa domin tattauna martaninta kan mutuwar mutane akalla 27 da suka yi kokarin ratsa mashigar ruwan da ke tsakanin kasar da Birtaniya wato Calaise a ranar Laraba, a wani karamin jirgin kwale-kwale na roba.
Mutne biyu da suka tsira daga hadarin na cikin mawuyacin hali a asibiti. Ana ganin kwale-kwlen ya kife ne, inda sai daga baya ne wani masunci ya ga da yawa daga cikin mutanen da ke cikin jirgin a kan ruwa.
Ana ganin wannan hadarin shi ne mafi muni a mashigar tun bayan da 'yan ci rani suka fara ketarawa a kananan kwale-kwale a 'yan shekarun da suka gabata.

Asalin hoton, AFP
Har zuwa yanzu dai babu wata masaniya ta sosai game da 'yan ci ranin da suka gamu da wannan hadari na kifewar jirgin ruwan na roba, wanda ake buga wa iska ko kuma dalilin da ya sa jirgin ya kife.
Ministan cikin gida na Faransa, Gerald Darmanin, ya bayyana kwale-kwalen da suke tafiyar a ciki da cewa yana da hadari kwarai.
Kwale-kwale ne yawanci ake yi domin satar shigar da mutane a wannan mashiga ta teku da ke tsakanin Faransar da Birtaniya.

Asalin hoton, AFP
Ministan ya ce an ga jirgin ya sace sosai.
Tuni dai aka bude bincike a kan irin tuhumar da za a yi kan kokarin satar shigar da mutane da kisan kai, a cewar ministan. An damke mutane hudu da ake ganin suna da alaka da lamarin.
A ranar Alhamis gwamnatin Faransar za ta yi wani taro domin tsara irin martanin da za ta yi game da lamarin.
Shugaba Macron ya lashi takobin yin duk abin da zai iya wajen ganowa da kuma gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin a gaban shari'a

Asalin hoton, AFP
A wata sanarwa shugaban ya ce, ''ba zan bari mashigar ta zama wata makabarta ba.
Abin da har kullum ake tsoro da fargaba shi ne ketara wannan ruwa abu ne da zai iya kai wa ga irin wannan hadari.
Ma'aikatn agaji da 'yan sanda a ko da yaushe suna gargadi a kai. Kuma 'yan ci-rani sun san da haka
Wannan harka ce da masu satar shigara da mutane ke samun kudi sosai. Amma kuma mutnen da ake shigarwa ne ke dandana kudarsu idan ta baci.











