Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ɗalibai 1,440 aka sace a hare-haren da aka kai makarantu 25 a Najeriya'
Wani rahoton Asusun UNICEF ya ce a Najeriya an kai hare-hare guda 25 kan makarantu zuwa yanzu, inda aka sace ɗalibai fiye da 1,400.
Rahoton ya ce ƙananan yara fiye da dubu 21 ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta tantance an ɗauke su aiki a matsayin mayaƙa a yankunan Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bankaɗo cewa daga shekara ta 2016, yankin Afirka ta Yamma da na Tsakiya sun sha samun adadi mafi yawa na rahotannin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tantance kan gagarumin take haƙƙin ƙananan yara a lokacin rikice-rikice.
Rahoton na UNICEF ya zargi dakarun tsaro da ƙungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai da ci da gumin ƙananan yara a yankunan biyu.
Asusun UNICEF ya ce bayan ƙananan yara sama da dubu 21 da aka ɗauka a matsayin mayaƙa akwai kuma ƙananan yara fiye da 2, 200 da aka yi wa cin zarafin lalata.
An kuma sace ƙananan yara sama da 3,500, sannan an kai hari 1, 500 kan makarantu da asibitoci a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya a cikin shekara biyar ɗin da ta wuce.
A cewar rahoton wani rikici da ya yi ƙamari a arewa maso gabashin Najeriya tsawon shekara 12 yanzu, ya zama sanadin kashe dubban yara da nakasa wasu da sacewa da raba wasu da gidajen iyayensu, baya ga waɗanda aka keta wa haƙƙi.
UNICEF ya ce tun shekara ta 2005, duk ɗaya a cikin huɗu na wani gagarumin take haƙƙin ƙananan yara da aka samu a duniya, an aikata shi ne a yankin Afirka ta Yamma ko kuma Afirka ta Tsakiya.
Rahoton ya ce a bara kawai, ƙananan yara sama da 6, 400 ne a cikinsu kuma kashi 32 cikin dari 'yan mata ne aka keta wa haƙƙi a yankunan na Afirka.
Babbar Jami'ar UNICEF a Maiduguri Phuong T. Nguyen ta ce ƙananan yaran Najeriya, ko dai kai tsaye an kai musu hari ko kuma tsautsayi ya sa an ritsa da su a wani hari, sanadin taɓarɓarewar tsaron da ake ci gaba da gani a faɗin ƙasar.
A cewarta, wannan, ba abu ne da za a lamunta ba, inda ta kara da cewa, ''Wannan muhimmin rahoto ya nuna tsananin keta haƙƙin ƙananan yara a Najeriya da kuma a fadin Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.
Lamarin da ta ce dole ne dukkan ɓangarori su kawo ƙarshensa.
''Wajibi ne'' in ji ta, ''ƙananan yara su samu zarafin girma, su yi ilmi, su samu aikin yi, kuma su ba da gudunmawarsu ga kyakkyawar makomar wannan ƙasa.''
''Hakan kuma zai samu ne kawai idan an kare ƙananan yara daga tarzoma da kuma mummunan tasirin rikice-rikice.''
Rahoton ya kuma nuna cewa manya-manyan matsalolin jin ƙai na ci gaba da faruwa a faɗin Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.
Abin da ke faruwa a Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo da matsalolin da ke buƙatar ɗaukin gaggawa a tsakanin ƙasashe ciki har da rikice-rikice a Tsakiyar yankin Sahel da yankin Tafkin Chadi na da gagarumar illa ga rayuwar ƙananan yara da al'ummomi.