China na shirin daina bai wa yara 'yan makaranta aikin gida

Kafar yada labaran China ta rawaito cewa an gabatar da kudurin dokar da zai daukewa yara 'yan makaranta tarin aikin gida da malamai ke ba su.

An bukaci iyaye su tabbatar y'ya'yansu sun samu isasshen lokacin motsa jiki da hutawa, su kuma rage yawan amfani da na'ura mai kwakwalwa.

A watan Agusta da ya wuce ne gwamnatin China, ta haramta yi wa dalibai 'yan shekara shida da bakwai yin jarabawa.

Jami'ai sun yi gargadin cewa, lamarin na cutar da lafiyar jiki da kwakwalwar daliban. Ko a shekarar da ta gabata, an gabatar da wasu jerin matakai da ya kamata a dauka domin ragewa yara nacewa na'ura mai kwakwalwa, d wasu daga cikin fitattun al'adun China.

An gabatar da mataki na baya-bayan nan a ranar Asabar, wanda kwamitin da ke sa'ido kan fannin ilimi ya gabatarwa ma'ikatar ilimin kasar.

Kawo yanzu ba a wallafa yadda cikakkiyar dokar za ta kasance ba, sai dai kafafen yada labarai na ce wannan wata dam ace ga iyaye domin su karfafawa yaransu gwiwar yin wasu abubuwan na daban.

Haka kuma gwamnatocin jihohi ne za su samar da isassun kudaden da za a kirkiro wasu sabbin abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum a manhajar ilimi.

Tuni mutane suka fantsama shafukan sada zumunta da muhawara su na bayyana ra'ayin su kan wannan doka.

Shafin sada zumunta na Weibo ya cika da sakwannin jinjina ga hukumomi kan matakin da suka dauka musamman iyaye.

Wani uba ya wallafa tambaya da aka wallafa a jaridar South China Morning Post cewa: "Ina zuwa wajen aiki daga karfe 9 na Safiya zuwa 9 na dare a kwanaki 6 na mako, amma duk da haka da zarar na dawo gida da daddare, dole sai na taimakawa yara da yin aikin gida?

"ba zai yiwu ku wahalar da ma'aikata ba sannan, sannan kum ku ce su kula da yara."

A watan Yuli ne hukumomi a birnin Beijing, su ka rufe shafukan da ke koyar da yara 'yan makaranta darusa ta yanar gizo, bayan gano irin makudan kudaden da suke samu da sunan koyarwa da kuma ke janyowa wasu daga cikin daliban rashin isasshe lokacin hutu bayan dawowa daga makranta.