Tamowa ka iya kashe yara kusan 300,000 a Najeriya a 2021 - UNICEF

    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bayyana matukar damuwa dangane da lafiya da kuma halin rayuwar kananan yara fiye da muliyan 10 da ake hasashen za su yi fama da matsananciyar matsalar karancin abinci mai gina jiki wato tamowa a shekara ta 2021 a wasu kasashe galibinsu na Afirka.

Asusun na UNICEF ya ce akwai fargabar dubun-dubatar kananan yara musamman 'yan kasa da shekara biyar da haihuwa za su rasa rayukansu a irin wadannan kasashe.

Kasashe da lamarin ya shafa sun hada da Najeriya, Jamhuriyyar Nijar, Burkina Faso, Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo (DRC), Sudan ta Kudu, da kuma Yemen.

Girman matsalar a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana tsammanin yara fiye da 800,000 ne za su yi fama da matsananciyar matsalar rashin abinci mai gina jiki wato tamowa a 2021 a arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan adadi ya hada da yara 300,000 dake fuskantar barazanar rasa rayukansu sanadiyyar wannan matsala.

Duk da girman matsalar da ake fuskanta a yankin arewa maso gabashin Najeriya musamman jihar Borno da Adamawa da Yobe inda ake fama da rikicin Boko, UNICEF ya ce matsalar tamowa da ake fuskanta a yankin arewa maso yammacin kasar ta fi ta arewa maso gabas.

A cewar wata sanarwa da reshen na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, jihohin Sokoto da Kebbi dake arewa maso yamma na cikin wuraren da aka fi fama da matsalar tamowa.

Misali a jihar Kebbi kashi 66 cikin 100 na kananan yara na fama da tamowa, wanda ke nufin adadin ya fi na jihar Borno da kamar kashi 20 cikin 100.

Haka nan a jihar Sokoto wadda ita ma ke arewa maso yamma, kashi 18 cikin 100 na fama da matsalar kanjamewa, yayin da kashi 6.5 na fuskantar matsananciyar kanjamewa - duka saboda rashin abinci mai gina jiki.

Mene ne ya janyo matsalar?

Hukumomi da kungiyoyin agaji na cewa akwai matsaloli da dama da suka jefa kananan yara cikin matsancin halin rayuwar a kasashe da dama.

Asusun UNICEF ya ce tashe-tashen hankula, da yake-yake, da karancin damar samun abinci mai gina jiki, da talauci na daga cikin matsalolin da ke haddasa karancin abinci da ake fuskanta a tsakanin jama'a da kuma matsalar tomowa dake addabar kananan yara.

Haka nan ya ambaci rashin ingantattun ayyukan kiwon lafiya da samar da ruwan sha da tsaftar jiki da ta muhalli, a matsayin wadansu dalilan.

Ambaliyyar ruwa da aka fuskanta a wasu yankuna, da kuma annobar korona wato COVID-19 a 2020 su ma sun kara ta'azzar matsalar.

Daraktar Zattaswa ta UNICEF Henrietta Fore ta ce duka wadannan matsalolin sun sanya matsalar karancin abinci mai gina jiki ta zamo 'bala'i.'

Ta kara da cewa gidaje wadanda dama da kyar suke iya ci da yaransu, yanzu suna gab da fadawa cikin bala'in yunwa, kuma bai kamata a manta da su ba.

Dangane da batun rashin tsaro, a arewa maso gaabshin Najeriya dai, an kwashe fiye da shekara 11 ana fama da rikicin Boko Haram inda matsalar ta raba muliyoyin mutane da muhallansu.

A yankin arewa maso yamma kuma aka kwashe shekaru da dama ana fama da matsalar 'yan bindiga masu kashe mjutane da kuma garkuwa da mjutane domin neman kudin fansa, kuma a nan ma mutane da dama sun yi hijira daga kauyuka da garuruwansu.

Wasu kasashe da matsalar ta shafa

A Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo kananan yara kimanin muliyan uku da 300,000 ne ake fargabar za su yi fama da tamowa a 2021.

A Sudan ta Kudu kuma adadin yara da matsalar za ta shafa zai iya kaiwa muliyan daya da 400,000. Kimanin 292,000 za su kasance masu matsananciyar tamowa.

A kasashen yankin tsakiyar Sahel kamar Nijar da Mali da Burkina Faso, karuwar tashin hankali da gudun hijira da tasirin sauyin yanayi da dai sauransu, za su jefa kananan yara kusan 3,000 000 cikin matsalar tamowa, cikinsu kuma 890,000 za su kasance masu matsananciyar tamowa.

Hakazalika a kasar Yemen, ana fargabar kananan yara fiye da 2 000 000 ke fama da karancin abinci mai gina jiki, kusan 358,000 kuma daga cikinsu na fama da matsalar tamowa mai tsanani.

Mene ne ya kamata a yi don dakile matsalar?

Asusun na UNICEF na kira ga masu ruwa da tsaki a ayyukan jin kan bil-Adama da kuma kasashen duniya da su gaggauta fadada damar jama'a ta samun abinci mai gina jiki, da kiwon lafiya da ruwan sha da tsaftar jiki da ta muhalli.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma ce magance talauci, da ilmantar da iyaye mata da masu kula da kananan yara kan yadda za su gano alamomin tamowa da kuma yadda za su dauki matakan kiyayewa, za su taimaka gaya.

Tabbatar da tsaro da wadata kasa da abinci na daga cikin wasu hanyoyin da masana ke ganin za su taimaka wajen shawo kan matsalar ta karancin abinci.

Duk da kalubalen da ake fuskanta na annobar korona, UNICEF ya ce ya taimaka wa kananan yara da dama a sassa daban-daban na duniya a 2020 ciki har da yankuna masu wahalar zuwa.

To amma asusun ya ce akwai bukatar bayar da tallafin kudi dala biliyan daya domin taimakawa da nufin ceto kananan yara a kasashe da matsalar ta yi kamari a duniya a 2021.