Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
COP26: Karairayin da ake yadawa game da sauyin yanayi
- Marubuci, Daga Rachel Schraer da Kayleen Devlin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Masu binciken ƙwaƙwaf na BBC
A daidai lokacin da shugabannin duniya suka taru a Glasgow domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi domin daƙile matsalalolin sauyin yanayi, an yi ta samun labarun ƙarya kan sauyin yanayin waɗanda aka yaɗa a shafukan sada zumunta.
Masana kimiyya sun bayyana cewa musanta sauyin yanayi da ake yi a yanzu ya fi mayar da hankali ne kan illolin ɗumamar yanayi da yadda za a shawo kan matsalar fiye da fitowa a ƙaryata lamarin.
Mun tsaya mun yi duba kan wasu daga cikin muhimman iƙirarin da aka yi kan batun sauyin yanayin da kuma abubuwan da hujjojin suka ce.
Ikirari na farko: Ƙarancin fitowar rana zai dakatar da ɗumamar yanayi
Mutane sun daɗe suna ikirarin haka ba daidai ba, kan cewa yanayin zafin da aka yi fama ɗaruruwan shekarun da suka gabata na daga cikin abubuwan da ake fuskanta a duniya a al'adance, ba wai abin da ɗan adam ke jawowa ba ne.
Amma a cikin ƴan watannin nan, mun ga sabon nau'i na irin wannan gardamar.
Dubban abubuwan da aka wallafa a shafukan sada zumunta da ɗaruruwan mutane suka samu gani a shekarar da ta gabata, an yi iƙirarin cewa ƙarancin fitowar rana zai sa a samu raguwa a yanayin zafi ba wai sai ɗan adam ya yi wani abu ba.
Amma ba wannan ba ne abin da hujjoji suka nuna ba.
Ƙarancin fitowar rana wani lamari ne da ita kanta rana ba ta bayar da hasken da ake buƙata a lokacin da take fitowa ba.
Bincike ya nuna cewa akwai wasu lokuta da rana za ta fuskanci naƙasu a wannan ƙarnin, amma hakan zai ja a samu sanyi da maki 0.1 zuwa 0.2 a ma'aunin celcius.
Mun san cewa ƙaruwar da aka samu a yanayin zafi ba wai ya samo asali ba ne daga sauyin yadda rana ke fita ba sakamakon sararin samaniyar da ke kusa da duniyarmu na da ɗumi, haka kuma sararin samaniyar da ke kusa da rana - yana da sanyi.
Gurɓatattun iska kamar irin su carbon dioxide musamman wadda ake samu daga fetir ɗin da mutane ke ƙonawa na riƙe zafin da zai shiga sararin samaniyar da ke kusa da rana.
Idan sauyin da ake samu na yanayin zafi ana samun shi sakamakon rana, da kuwa yanayin gari zai zama cikin zafi da sanyi a lokaci ɗaya.
Iƙirari: Ɗumamar yanayi yana da kyau
Saƙonni da dama da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun yi iƙirarin cewa dumamar yanayi zai sa wasu sassa da ɗan adam ba ya rayuwa ya zama yana iya rayuwa, haka kuma sanyi ya fi kashe mutane fiye da zafi.
Waɗannan iƙirarin da aka yi wasu na daukar su da muhimmanci inda suke ƙyale wasu abubuwa game da su da ke ƙaryata su.
Alal misali, da gaske ne wasu wurare masu sanyi na duniya za su zama suna da sauƙin zama na ɗan wani lokaci.
Amma a irin waɗannan wuraren, zafi zai iya janyo ruwan sama mai ƙarfi, wanda hakan zai iya shafar yadda mutane ke zama a wurin haka kuma lamarin zai shafi noma.
Haka kuma wasu sassa na duniya za su zama ɗan adam ba zai iya rayuwa a cikinsu ba sakamakon yadda aka samu ƙarin zafi kamar yadda aka samu a ƙasar Maldives.
Akwai mutane kaɗan da aka samu sun mutu sakamakon sanyi. Kamar yadda aka wallafa wani bincike a mujallar Lancet tsakanin shekarar 2000 zuwa 2019, mutane sun fi yawa sakamakon yanayi mai zafi .
Haka kuma, ƙaruwar da ake samu a irin mace-macen da ake samu sakamakon zafi zai soke adadin rayukan da aka ceto.
Kwamitin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa kan batun sauyin yanayi ya bayyana cewa "barazanar da ke da akwai ga lafiya sakamakon sauyin yanayi...an yi hasashen cewa za ta ƙaru da ɗumamar yanayi da maki 1.5 a ma'aunin salshiyos".
Iƙirari: Sauyin yanayi zai jawo wa mutane talauci
Wani iƙirari da wasu da ba su goyon bayan daƙile matsalolin sauyin yanayi suna bayyana cewa makamashi na al'ada yana taimakawa wajen haɓaka tattalin arziki.
Sun bayyana cewa taƙaita amfani da makamashin zai jawo durƙushewar tattalin arziki da kuma ƙara tsadar rayuwa da kuma jawo matsaloli ga talaka.
Amma ba haka lamarin yake ba.
Makamashi ne motoci suke amfani da su, haka masana'antu , wanda hakan ya sa bil'adama fiye da shekara 100 suka sa abubuwa suka yi sauri da sauƙi wanda a da ba a samu hakan ba.
Wannan ya ja hankalin jama'a suka iya sayar da kayayyaki da kuma sayen ƙarin kayayyaki da kuma zama masu arziƙi.
Amma daina amfani da gawayi ba yana nufin komawa zamanin amfani da baro da amalanke ba ne- a yanzu muna da sabbin fasahohi da za su iya yin irin waɗannan ayyuka.
A wurare da dama, wutar lantarki da ake samarwa mai tsafta - wadda ake samu ta hanyar iska ko hasken rana misali - ya fi sauƙi kan yadda ake samar da lantarki ta hanyar gawayi ko mai ko kuma gas.
A ɗayan ɓangaren kuma, binciken ya yi hasashen cewa idan ba mu yi wani abu ba kan sauyin yanayi ba zuwa 2050, tattalin arziƙin duniya zai ragu da kashi 18 cikin 100 sakamakon irin illar da da bala'o'i za su yi wa gidaje da rayuka da kasuwanci da kuma samar da abinci.
Irin wannan bala'in zai fi ƙamari ne a ƙasashen duniya waɗanda suka fi talauci.
Iƙirari: Makamashi mai tsafta ba shi da tabbas
Saƙonnin da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun yi iƙirarin cewa rashin samar da makamashi mai tsafta zai iya jawo rashin wuta wanda hakan ya zagaya a shafukan sada zumunta, kuma hakan ya faru ne bayan da aka samu matsalar lantarki a Texas da ke Amurka a bara, lamarin da ya ja mutane miliyoyi suka zama cikin rashin wuta da kuma sanyi.
Irin wannan labarin wanda kafofin yaɗa labarai suka ɗauka a Amurka, sun ɗora alhakin hakan bisa kuskure kan turakun da iskar ke juyawa waɗanda ke samar da lantarkin.
"Ɗaukewar wutar lantarki na faruwa ne sakamakon rashin ingancin samar da lantarkin da yanayin rarraba ta," in ji John Gluyas, babban darakta na kamfanin cibiyar makamashi ta Durham.
Ya bayyana cewa iƙirarin da ake yi cewa tsaftataccen makamashi na jawo ɗaukewar wuta "maganar kawai ce....Venezuela na da mai sosai kuma ana ɗauke wuta".