COP26: Shin ko za a iya takaita yawan naman da ake ci?

Ana gudanar da taro kan sauyin yanayi na COP26 a Glasgow - daya daga cikin manyan tarukan da aka taba gudanarwa a duniya a kan yadda za a magance matsalar dumamar yanayi.

Wakilin BBC kan News Reality Check Chris Morris da wakilin muhalli Matt McGrath sun amsa wasu tambayoyinku.

Kuna iya aika tambaya ta amfani da fom a kasan wannan shafin.

Shin akwai hanyar da za a bi don tilastawa kasashe a Majalisar Dinkin Duniya, musamman China da Indiya, rage gurbatacciyyar iskar da suke fitarwa nan da shekarar 2050? Shin za a iya amfani da takunkumi ko takunkumin kasuwanci a kansu? Diana Butungi, Kampala

Kasashe kalilan ne kawai suka aiwatar da alkawuran da suka yi. Yawancin alkawuran da aka yi na kasa ba makasudi ne ba, amma akwai fatan cewa yayin da ake ci gaba da samun ci gaba a kan wannan batu, zai ba da kwarin gwiwa ga wasu su bi.

Duk da cewa za a iya daukar sanyawa kasashe da ke jan kaa a kan wannan batu takunkumi ko takunkumin kasuwanci amma watakila matakin ba zai yi tasiri ba. Manufar tarurruka kamar COP26 ita ce kokarin karfafa hadin gwiwar kasashen duniya.

Har ila yau, ba dai dai ba ne a dora wa kasashe irin su Indiya da China alhakin fitar da mafiya yawan hayaki mai gurbata muhalli, duk da cewa kasar Sin ce ta fi kowace kasa fitar da hayaki mai gurbata muhali, a duniya a halin yanzu, kuma Indiya ce ta uku.

Hakanan yana da mahimmanci a yi la'akari da rawar da ƙasashen Turai da Amurka suka taka a baya waɗanda ke da alhakin fitar da hayaƙi mai gurbata muhalli fiye da China ko Indiya.

Illolin da hayaki mai gurbata muhalli ya janyowa yanayi za su dade na tsawon daruruwan shekaru, kuma kasashen duniya masu arziki sun amince da cewa su ne su ke da alhakin farko na tunkarar sauyin yanayi.

Shin akwai shirye-shiryen da aka tanadar wa gwamnatoci da ƙasashe don saka hannun jari a cikin fasahohin rage hayaki mai gurbata muhali ? Idan ba haka ba, me yasa? Bernath Bence, Netherlands

Chris Morris ya rubuta:

Matsalar da ake fuskanta ita ce fasahar da ake da ita yanzu ba za ta iya matukar rage yawan hayaki mai gurbata muhali da ake fitarwa ba da za ta sa a samu gagarumin bambanci a cikin shekaru goma lwanda shi ne lokacin da ake bukatar samun matukar raguwa a hayakin da k gurbata muhali.

Misali Burtaniya ta ware fam biliyan 1 ga asusun samar da wuararen da za a rika adana hayaki mai gurabata muhali watau CCS, tare da burin ganin cewa ta rage tan goma na hayaki mai gurbata muhali da ta ke fitarwa nan da shekarar 2030. An yi kiyasin Burtaniya ta fitar da tan 450 na hayaki mai gurbata muhali a shekarar 2019.

Yadda gomnatocci su ke zuba jari a duniya ya danganta. Kasashe kamar Saudi Arabia da Ostiraliya suna dogaro sosai kan hayakin na CCS don ba su damar ci gaba da samar da makamashin mai a nan gaba, amma hakan na nufin bunkasa fasahar ta hanyar da ba a tabbatar ko zai yi tasiri ba.

Ta yaya kayayyakin noma kamar shinkafa da sukari ke taimakawa wajen karuwar hayaki mai gurbata muhali? Me za mu iya yi don taimakawa rage fitar da hayaki mai gurbata muhali ? Ng Wee Meng, Singapore

Chris Morris ya rubuta:

Yawancin nau'ikan noma suna haifar da hayaƙin mai gurbata muhali .

An yi intifakin cewa naman sa shi ne abinci da ake samarwa a duniya da ke sa a fitar da hayaki mai gurbata muhali, amma akwai ana samun hayaki daga sukari da shinkafa - waɗannan suna da alaƙa da abubuwa kamar sare bishiyoyi, abincin dabbobi, makamashin da ake amfani da shi wajen sarrafawa da sufuri, da kuma tattara kaya.

Wani bincike ya yi kiyasin cewa shinkafa, alal misali, tana samar da kwatankwacin kilogiram 4 na hayaki mai gurbata muhali ga kowace 1kg ta shinkafar da ake samarwa. Idan aka yi la'akari da cewa ana samar da tan miliyan 755 na shinkafa duk shekara a duniya, wato hayaki mai gurbaa muhali mai yawa sosai. A daya bangaren kuma, shinkafa wata muhimmiyar abinci ce ga biliyoyin mutanen duniya.

Hanya mafi kyau don taimakawa rage fitar da hayaki ita ce a yi ƙoƙarin tabbatar da cewa kuna cin abinci wanda aka samar da shi yadda ya kamata - kodayake mutane da yawa ƙila ba su da karfin yin haka.

Shin ko rageyawan cin nama da tafiye-tafiye a jirgin sama za su yi tasiri ? Tambayar da wani da bai bayyana sunansa ba ya turo .

Chris Morris ya rubuta:

Cin nama (musamman naman sa) da tafiya ta jirgin sama duka suna yi wa muhalli illa.

Cin burodin da aka yi da hada da nama da ake kira hamburgers guda ɗaya ko biyu a mako har tsawon shekara guda yana haifar da adadin hayaki mai gurbata muhali iri ɗaya kamar dumama gida guda Burtaniya na tsawon kwanaki 95.

Kuma jirgin saman da ya tashi daga London domin zuwa New York yana fitar da kusan tan 0.67 na hayaki mai gurbata muhali. Wannan shine kashi 11% na matsakaicin hayaki na shekara ga wani a Burtaniya.

A rubuce takaita yadda ake cin nama ko tafiya da jirgin sama zai kawo canji, amma 'yan siyasa ba su da aniyyar ganin cewa hakan ta faru . Maimakon haka, an mayar da hankali kan sauya halayyar mutane.

Kwamitin sauyin yanayi na Burtaniya - wanda ke ba gwamnati shawara - ya ba da shawarar cewa mutane su rage cin nama da madara da kashi 20 cikin 100 nan da shekarar 2030, sannan kuma a rage kashi 35 cikin 100 nan da 2050. An kuma bukaci mutane da su yi tunanin rage tafiye tafiye da jiragen sama.

Shin me yasa ba za a kafa asusun taimakawa kasashe masu tasowa wajan rage yawan hayaki mai gurbata muhali ? daga Robert Patterson, Darlington

Chris Morris ya rubuta

Wannan shi ne wani bangare na abin da ake tattaunawa a yanzu a taron kudi kan sauyin yanayi .

A shekarar 2009 kasashe masu karfin tattalin arziki sun ce za su samar da dala biliyan 100 a kowace shekara ga kasashe masu tasowa nan da shekarar 2020. Sai dai sun kasa cika alkawarin da suka dauka, kuma a yanzu sun nuna cewa za su cimma wannan burin ne kawai a shekarar 2023.

Kasashe masu fama da talauci na bukatar wannan kudi domin su taimaka wajen shawo kan illolin sauyin yanayi da suke fuskanta.

Sai dai suna bukatar kudin domin su tabbatar cewa tattalin arzikinsu ba su dogara a kan hayaki mai gurbata muhali ba ya yin da suke kan hanyarsu ta rage yawan hayakin da su ke fitarwa da ke gurbata muhali.

Idan mutane ne ke janyo sauyin yanayi , wani mataki aka dauka don rage yawan jama'a? Daga Gaye Schmidt, Perth, Ostiraliya

Chris Morris ya rubuta:

Yawan jama'a ba shine tushen sauyin yanayi ba. Maimakon haka, yawan fitar da hayaki mai gurbata muhali ke dumama duniya. Kuma kashi ɗaya cikin ɗari na al'ummar duniya da ke kasashe masu arziki ne ke da alhakin fitar da hayaƙi mai gurbata muhali fiye da kashi hamsin cikin dari na kasashe mataulata.

Gaskiya ne a ce yawan al'ummar duniya ba zai iya ci gaba da karuwa ba har abada, saboda akwai iyakataccen adadin albarkatu. Amma yawan amfani da abinci ya taka rawa wajen sauyin yanayi fiye da karuwar yawan al'ummar duniya.

Menene tasirin adadin methane akan sauyin yanayi? Maya Yossifova, Vienna, Austria

Matt McGrath ya rubuta:

Methane iskar gas ce mai gurbata muhali, wacce ke fitowa daga tushe guda biyu, kamar wuraren masu dausayi da kwari, haka nan ta hanyar ayyukan dan Adam kamar noma, amfani da man fetur da wuraren zubar da kasa.

A cewar Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya, yawan methane da ke cikin sararin samaniya ya karu sosai a 2021.0.

Wane kwarin gwiwa mu ke da shi game da tasirin taron COP26 yayin da duniya a kasa hada kai wajan rarraba alluran rigakafi ? Mahesh Nalli, London

Matt McGrath ya rubuta:

Akwai kamanceceniya tsakanin annobar da rikicin yanayi, amma wasu mahimmin bambance-bambancen ma.

Kamar yadda muka gani a cikin watanni 18 da suka gabata, kasashe na iya kiyaye Covid ta hanyar takaita zirga-zirgar mutane a kan iyakokinsu.

Sai dai wannan tsarin a zai yi tasiri ba a kan hauhawar yanayin zafi da ke shafar ƙasashe masu arziki da matalauta .

Yayin da za a iya magance matsalar rashin dadaito wajan rarraba allurar rigakafi a cikin gajeren lokaci da kudi, amma matsalar yanayi tana buƙatar sake tunani da sake fasalin kusan kowane bangare na rayuwarmu, daga makamashi zuwa abinci zuwa tufafi.

Shin da gaske taron COP26 na buƙatar mutane 25,000 a wurin? Za su a samu karin hayaki mai gurbata muhali , don haka me yasa a zaa yi abubuwa da yawa ta shafi intanet ba? Daga David, Birmingham

Matt McGrath ya rubuta:

Ana ganin annobar korona a ba Majalisar Dinkin Duniya damar amfani da fasaha don tattaunawa , kuma an yi ƙoƙarin yin hakan gabanin taron sauyin yanayi a watan Yuni, wanda ya gudana na tsawon makonni uku.

Abin takaici shine, kwaliya bata biya kudin sabulu ba - ƙalubalen banbancin a lokacin kasashen duniya da kuma na fasaha sun sa ya zama kusan ba zai yiwu ba ga ƙasashe masu karamin karfi, kuma ba bu wani abin azo gani kuma an dakatar da bada shawara.

Sakamakon haka, ƙasashe masu tasowa da dama suka dage wajan ganin an yi taron ido da ido a taron sauyin yanayin . Suna ganin cewa ya fi sauki a yi watsi da muryoyin saboda tangarda a shafin intanet

Har ila yau, sun gabatar da matsalolin da suke fuskanta sanadin sauyin yanayi ga ƙasashe masu arziki wanda wani abu ne mai muhimanci da za su so su ji da kansu.

Akwai shaidar da ta nuna cewa wannan yana aiki. A cikin 2015, kasancewar kasashe tsibirai da ƙasashe da sauyin yanayi ke tasiri shi ne ya sa kasashen duniya su ka yi alkaurin rage dumamar yanayi da maki daya da digo biyar a yarjejeniyar da aka cimma a Paris.

Wadanne tambayoyi ku ke da shi kan sauyin yanayi ?

Ku yi amfani da fom da ke kasa wajan rubuta tambayoyinku