Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiyar jarirai: Yadda yi wa jarirai tausa ke cetar rayuwarsu
- Marubuci, Daga Kamala Thiagarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
Tausar jarirai wani lamari ne da aka jima ana yinsa a Kudancin Asia shekaru ɗaruruwa. A yanzu masana kimiyya sun soma gano yadda wannan tsohuwar al'ada ke ceton rayuka.
A wani dare mai sanyi a watan Oktoba, Renu Saxena ta dawo daga asibiti da jaririyarta a birnin Bengaluru da ke kudancin Indiya. Abin ya dame ta ganin yadda ƴarta take kamar ta kare ga ta siririya ga jijiyoyi ɓaro-ɓaro sun fito ana gani. An haife ƴar da wuri lokacin haihuwarta bai yi ba, an haife ta cikinta na makonni 36 kuma tana da nauyin kilo 2.4
Iyalan Saxena sun buƙace ta da nan take ta soma wata tsohuwar al'ada ta ƙasar Indiya da ake yi wa sabbin haihuwa domin su warware: wato tausar da ake yi musu kullum. Sai dai likitocin da ke duba ƴar na ɗar-ɗar da wannan lamarin inda suka ce mahaifiyar ta dakata har sai yar ta ɗan ƙara nauyi kafin ta soma yi mata tausar.
Amfanin nau'in tausar jariraida ake yi a Kudancin Asia
Bincke iri-iri da aka yi a baya ya nuna cewa amfani da mai wajen tausa idan aka yi tausar da kyau zai iya haɓaka girman jarirai da kuma kare su daga kamuwa daga cututtuka da kuma rage mutuwar yara da kashi 50 cikin 100.
Iyayen da suke da ra'ayin irin wannan tausar, akwai buƙatar su tattauna da likitocinsu tukuna, domin tabbatar da cewa yin hakan babu wata matsala ga jariransu.
Ga iyalan da suke ɗaukar wannan daɗaɗɗiyar al'ada da muhimmanci, bincike ya gano abubuwan da aka lura da su. Saxena, wadda tsohuwar shugabar wani rukuni na tallace-tallace ce, asali daga jihar Uttar Pradesh take ta Indiya, kuma jihar ta yi fice wajen yi wa uwa da jaririnta tausa bayan haihuwa. Danginta sun shafe shekaru aru-aru suna yin hakan.
Shawarar uwa
"A lokacin da muka soma girma, mahaifiyarmu na yawan faɗa mana yadda ta yi saurin farfaɗowa bayan ta haife ni, da ɗanta na uku da kuma yadda na yi saurin girma, inda ta ce duk sakamakon yadda ta rinƙa yi mani tausa ne tun bayan da ta dawo gida bayan ta haife ni," in ji Saxena.
Unguwarzoma ta nuna mata yadda za a rinƙa ɗumama man, ana sauyawa tsakanin man kwakwa da kuma na gyaɗa, inda za a bi a hankali wajen shafawa a jikin ƴar a kullum inda za a shafe minti talatin ana yi, bayan nan kuma sai a yi wanka na ruwan zafi.
"Mun soma ne a hankali daga kan cikin jaririyar inda muka faɗaɗa zuwa sauran sassan jikinta," in ji ta. "Inda a hankali muka rinƙa lanƙwasa hannayen suna tabo ƙafafuwa ana kuma taɓo kai domin fitar da duk wani iska."
Yi wa yara tausa na taimaka musu ta fannin lafiya da zai taimaka musu har su girma, kamar ydda masu bincike suka bayyana.
Amfanin tausa ga fata
"Fata ita ce ɓari mafi girma a jikin ɗan adam, sai dai ba mu cika ba gyaran fata muhimmanci ba idan ana batun lafiya," in ji Gary Darmstadt, farfesa ne a ɓangaren kula da jarirai a jami'ar koyon aikin likitanci ta Stanford.
A tafiye-tafiye na farko da ya yi zuwa Bangladesh da Indiya, Darmstadt ya lura da cewa musamman iyaye mata da kakanni mata, suna ɗaukar lokaci mai tsawo suna yi wa jarirai tausa.
"Abin ya bani sha'awa bayan da na gano cewa an shafe shekaru ɗaruruwa ana wannan al'ada, inda daga nan ne na fara bincike a kai," in j ishi.
A 2008, a wani bincike da aka yi kan jarirai bakwaini 497 da aka yi waɗanda aka rinƙa yi wa tausa a kullum a wani asibiti da ke Bangladesh, Darmstadt da kuma abokan aikinsa sun nuna cewa wannan tsohuwar al'adar kan ceto rayuka.
Rage yawan mutuwa
"Mun samu raguwa da kashi 40 cikin 100 a barazanar da ake da ita ta kamuwa da cututtuka haka kuma an samu raguwa da kashi 25 zuwa 50 cikin 100 a barazanar da ake da ita ta mutuwa wanda hakan abu ne mai kyau," in ji shi.
Cikin gwaje-gwaje da dama da aka yi, masu binciken sun gano cewa yawan yin tausar na taimakawa wajen gina microbiome - wanda wuri ne a jikin mutum da hanjinsa da ƙwayoyin cuta ke zama.
Mircobiome na taka muhimmiyar rawa wajen ƙara ƙarfin garkuwar jikin ɗan adam, ta hanyar zama wata makami da za ta yaƙi cututtuka.
"Jarirai waɗanda ba su samun abinci mai gina jiki waɗanda aka yi wa tausa da mai suna samun mircobiome wanda na daban ne," in ji Darmstadt. "Mai irin wannan na gyara fata wanda hakan ke yi wa ƙwayoyin cuta wahala su shiga jikin mutum ta fatar shi, inda idan suka shiga za su shiga jini ne su jawo mutum ya kamu da cuta."
Waɗannan abubuwan da aka gano na da fa'ida matuƙa ga jarirai bakwaini. "A bakwaini, katangar da ke tsakanin fata da cikin jikin ɗan adam ba ta aiki sosai wanda hakan kuma na ja ana rasa ruwan jiki ta fata.
Ruwa yana fita daga jiki cikin sauri kuma ruwan da ke fita yana da zafi. Hakan zai iya sa zafin jikin jariri ya yi ƙasa fiye da kima," in ji shi.
Idan zafin jikin mutum ya yi ƙasa sosai, hakan zai iya barazana ga lafiyarsa. "Yaro na rage kuzari matuƙa idan jikinsa na yaƙi da batun raguwar zafi. Wanda zafin zai iya taimakawa wajen watakila girmansa da sauran sassan jikinsa," in ji shi.
Haihuwar jariri kafin lokacinsa
A wani bincike da hr yanzu ba a wallafa shi ba wanda Darmstadt da kuma abokan aikinsa suka yi, masu bincike sun bi diddiƙin jarirai 26,000 ba wai waɗanda aka haifa bakwaini kawai ba, a arewacin jihar Uttar Pradesh.
Rabin su an yi musu tausa ne ta hanyar amfani da man sunflower da kuma man da aka yi da mustard. Masu binciken sun lura da cewa an samu ci gaba ta ɓangaren girman jarirai.
"Ganin cewa bbu wani tasiri na yawan mce-mace ga jariran da aka haifa masu madaidaicin nauyi, a cikin ƙananan jarirai, akwai raguwa da aka samu da kashi 52 cikin 100 na raguwar barazanar mutuwa," in ji shi.
Sauran masu binciken sun samu gano irin wannn fa'idar.