Jarirai 7 sun mutu a dare ɗaya a wani asibitin Zimbabwe

    • Marubuci, Daga Andrew Harding
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent, BBC News

A daren ranar Litinin aka haifi jarirai bakwai babu rai a wani asibiti da ke Zimbabwe bayan da aka gaza samun taimakon gaggawa wajen karbar haihuwar sakamakon rashin ma'aikatan jinya da ma likitoci a asibitin.

Ma'aikatan jinya dai na yajin aiki a kasar saboda rashin kayan kariya daga kamuwa da cutar korona da kuma wasu dalilan daban.

Wani likita ya ce mace-macen jariran da aka samu a ranar Litinin abin damuwa ne kwarai da gaske.

Bangaren lafiyar kasar dai na cikin tsaka mai wuya saboda matsalolin da suka shafi annobar korona.

Ana dai zargin cewa an yi sama da fadi wasu makudan kudade da aka ware wa bangaren lafiya a kasar, abin da ya sa aka kori ministan lafiya na kasar daga aiki kenan.

Wata takardar da manyan likitocin kasar suka rubuta wa gwamnati a kan korafinsu da kuma barazanar tafiya yajin aiki, ta nuna irin kalubalen da asibitocin kasar ke fuskanta musamman na rashin kayayyakin aiki da dai makamantansu.

Wani likita ne ya fara wallafa wa a shafinsa na Twitter cewa, muna rasa manyan gobenmu saboda jarirai na mutuwa a asibiti.

Wasu likitoci biyu sun tabbatar wa BBC cewa a daren ranar Litinin 27 ga watan Yuli, 2020, an yi wa mata masu juna biyu takwas aiki inda aka cire musu jariransu, amma guda bakwai daga cikin jariran babu rai sai guda kawai.

Suka ce, ba a kai wa matan taimakon da ya dace a kan kari bane shi ya sa aka rasa jariran, saboda yawancin matan suna da 'yan matsalolinsu da suke bukatar daukin gaggawa wajen haihuwa, amma ba a kai musu daukin ba.

Likitocin dai sun yi korafi a kan karancin kayan kariya da kuma maganin da ake baI wa wadanda suka kamu da ciwon jijjiga da kuma karancin jinin da ake sanya wa wadanda suka haihu suka zubar da jini.

Akwai ma'aikatan jinya wadanda ba su shiga yajin aikin ba, amma kuma ba za su iya aikin su kadai ba.

Likitoci na kokari sosai amma kuma sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.