Iraƙi: An yi yunƙurin kashe Firaiminista al-Kadimi a gidansa

Mustafa al-Kadhimi

Asalin hoton, Getty Images

Firaiministan Iraƙi Mustafa al-Kadimi ya ce ya sha da ƙyar kuma bai samu rauni ba a yayin wani hari da aka kai a gidansa da ke Bagadaza babban birnin Iraƙi.

Jami'an ƙasar sun shaida cewa an kai wa gidan Firaiministan wanda ke wani yanki na musamman da ke babban birnin ƙasar hari ta hanyar amfani da ƙaramin jirgi mara matuƙi da aka ɗora wa ababen fashewa.

A wani saƙo da Firaiminstan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya yi kira da kowa ya kwantar da hankalinsa tare da kame kai saboda samun zaman lafiya a ƙasar.

Rahotannin farko da aka fara samu daga ƙasar na cewa an kai Mista al-Kadimi asibiti bayan kai harin.

Jami'an ƙasar sun bayyana cewa aƙalla mutum shida ne suka samu raunuka a cikin jami'an tsaron firaiministan.

Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki nauyin kai wannan harin wanda aka kai a unguwar ta musamman wadda ke da manyan gine-ginen ma'aikatun gwamnati da kuma ofisoshin jakadanci.

An rantsar da Mista al-Kadimi a matsayin firaiministan ƙasar ne a watan Mayun bara, kuma a baya ya shugabanci hukumar leƙen asirin ƙasar.

A ƴan makonnin nan, magoya bayan haɗakar jam'iyyun siyasar ƙasar sun gudanar da zanga-zanga kusa da unguwar da gidan firaiministan yake.

Sun ta gudanar da zanga-zangar ne kan ƙin amincewa da suka yi da sakamakon babban zaɓen ƙasar wanda suka ce ba a bi ƙa'ida ba wajen gudanar da shi.

Sama da mutum 100 ne suka samu raunuka yayin arangamar da jami'an tsaron Iraƙin suka yi da masu zanga-zangar a makon da ya gabata.