Lionel Messi na son ya koma Barcelona

Lionel Messi ya ce ya na son ya koma Barcelona a matsayin darektan wasannin kungiyar a nan gaba.

Messi, mai shekara 34, ya bar Nou Camp a watan Agusta, bayan shearu fiye da ashirin, inda ya koma Paris St Germain.

Duk da cewa bai yi tunanin ritaya ba tukuna ''zan so na zama daraktan wasani a Barcelona a wani lokaci''.

Ya kuma kara da cewa ''Ban sani ba ko hakan zai kasance a Barcelona ko a wani wuri da ban.Idan akwai damar, zan so in koma in ba da gudummawa.''

A hirar da ya yi da jaridar Sport ta Spaniya, dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or shida ya ce ''A ko yaushe ina cewa zan so in taimaka wa kungiyar.

"idan akwai yiwwar, zan so in sake ba da gudummawa saboda kulob ne da nake so kuma zan so ya ci gaba da samun nasara da bunkasa, kuma ya ci gaba da kasancewa daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa mafi kyau a duniya.''

Ya kara da cewar ''Wannan shi ne abinda matata ke so kuma abin da nake so. Ban san lokacin da kwantiragina zai kare da PSG ba amma za mu koma Barcelona da zama."

Messi ya ci wa Barcelona kwallaye 672 , amma ya bar kulob din a lokacin da kwantiraginsa ya kare, saboda yawan basussukan da ake bin Barcelona ya sa ta kasa sabunta yarjejeniyar da ta cimma da shi.

Maganar ritayar ba ta cikin ajandarsa kuma ya ki cewa komai a kan ko zai buga wasa bayan gasar cin kofin duniya a Qatar da za a yi lokacin hunturu mai zuwa, inda zai cika shekara 35.

"Bayan duk abin da ya faru da ni, ina bin rayuwa sannu a hankali, in ji Messi.''Ban san abin da zai faru bayan gasar cin kofin duniya.

Messi ya yi watsi da maganganun da ake yi a kan cewa ya ki amincewa ya buga wasa kyauta a Barcelona, yana mai cewa ya yi duk abinda ya kamata don ci gaba da zama a kungiyar.

''Gaskiyar magana itace kamar yadda na bayyana lokacin da na tafi, na yi duk mai yiwuwa don na zauna,'' in ji shi.

Ba bu wani lokaci da suka nemi na buga wasa kyauta, sun ce na rage albashina da kashi 50 na yi hakan ba tare da wata matsala ba.''