Lionel Messi: Dan wasan zai koma kan ganiyarsa a kakar nan

Lionel Messi zai sake komawa kan ganiyarsa a tamaula kuma kyaftin din Barcelona na farincikin zama a kungiyar in ji koci Ronald Koeman.

Kyaftin din tawagar Argentina, mai shekara 33 ya kusan barin Camp Nou a bana, daga baya ya amince zai ci gaba da taka leda a Spaniya.

Kawo yanzu kwallo daya Messi ya ci wa Barcelona tun fara kakar bana ta 2020/21.

''Bani da wani korafi ko tantama kan rawar da Messi zai taka,'' in ji Koeman wanda zai ja ragamar Barcelona Gasar Champions League da Ferencvaros ranar Talata.

Kawo yanzu kwazonsa zai dunga karuwa. yau da gobe, yana cikin farinciki yana kuma son buga tamaula da yake shi ne kyaftin din kungiyar.

Messi yana kakar karshe ta yarjejeniyarsa a Spaniya zai kuma fuskanci Ronaldo a gasar Champions League da za su fafata rukuni daya da Juventus a kakar bana.

Rabonda Barcelona ta lashe Kofin Champions League tun 2015.

Wasannin Champions League da za a buga ranar Talata 20 ga watan Oktoba

  • Chelsea da Sevilla
  • Rennes da FK Krasnodar
  • Zenit St Petersburg da Club Brugge
  • Lazio da Borussia Dortmund
  • Dynamo Kiev da Juventus
  • Barcelona da Ferencvaros
  • Paris Saint Germain da Man United
  • RB Leipzig da Istanbul Basaksehir

Ranar Laraba 21 ga watan Oktoba

  • RB Salzburg da Lokomotiv Moscow
  • Bayern Munich da Atletico Madrid
  • Real Madrid da Shakhtar Donetsk
  • Inter Milan da Borussia Monchengladbach
  • Manchester City da FC Porto
  • Olympiacos da Marseille
  • Ajax da Liverpool
  • FC Midtjylland da Atalanta