Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Faransa ta dakatar da batun sanya wa Birtaniya takunkumi
Faransa ta dage barazanar da ta yi ta kara tsaurara matakan binciken fito a kan hajojin da ake shiga kasarta daga Birtaniya, tare da daukar matakai a kan jiragen ruwan Birtaniyar, a sabanin da suke fama da shi a kan lasisin kamun kifi bayan ficewar Birtaniyar daga Tarayyar Turai.
Da yake Magana da ƴan jarida a taron sauyin yanayi na duniya da ake yi a Glasgow, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasashen biyu suna tattaunawa, a don haka ba za a sanya wani takunkumi ba yayin da ake tattaunawa.
A ranar Alhamis ake sa ran Ministan Birtaniya kan Shirin ficewar kasar daga Turai zai je Paris.
Ƴan sa'o'i kadan ne kawai suka rage kafin Faransar ta sanya matakan da ta yi barazanar dauka a kan Birtaniyar kan wannan takaddama da suke ta yi, to amma kwatsam sai Shugaba Macron ya dakatar da aniyar, ya sanya aya ko a ce wakafi.
Yana mai kafa hujja da cewa ai idan ana tattaunawa ba a maganar sanya takunkumi, kamar yadda ya gaya wa 'yan jarida a birnin na Glasgow.
Ya ce tuni ya riga ya gabatar da shawarwari domin yayyafa wa wutar rikicin ruwa, kuma yana sa ran ya ga Birtaniya a nata bangaren ta zo da nata shawarwarin.
Kakakin Birtaniya yace gwamnatin kasar a shirye take ta ci gaba da tattaunawa ta sosai, wadda ake bukata domin samun sasanto a kan jerin matsaloli masu wuyar sha'ani da ke tsakanin alakar Birtaniyar da Tarayyar Turai.
A ranar Alhmis ne, Lord Frost zai gana da Ministan Faransa na Tarayyar Turai Clement Beaune a Paris.
A makon da ya gabata ne Mr Beaune ya ce harshen da Birtaniya ke fahimta kawai shi ne na amfani da karfi.
Fadar gwamnatin Faransa ta ce ba wani takunkumi da za a sa, har sai an ga yadda ta kaya a bayan tattaunawar ta ranar Alhamis.
To amma anya yadda sauran manyan batutuwa na sabanin da ke a tsakaninsu da kuma siyasar da kowanne ke lasaftawa a bayan fage, suka damfara tare da kankane batun kamun kifi, a ce diflomasiyya za ta isa shawo kan wannan tsama da rashin yarda da ke a takanin kasashen biyu