Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Emmanuel Macron: Wani mutum ya gaura wa shugaban Faransa mari
Wani mutum ya gaura wa shugaban Faransa Emmanuel Macron mari a lokacin ziyarar da yake yi a kudu maso gabashin kasar.
A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Mr Macron yana tafiya zuwa wajen wani shinge lokacin balaguron da ya yi zuwa Tain-l'Hermitage da ke wajen birnin Valence.
Mutumin ya wanke Mr Macron da mari a fuska ne kafin jami'ai su yi hanzarin kai masa dauki. Daga nan ne aka janye shugaban.
Kafofin watsa labaran Faransa sun ce an kama mutum biyu bayan gaura wa shugaban kasar mari.
A yayin da aka mari shugaban kasar, an ji wasu suna ihu suna cewa "Allah wadaran akidar Macron".
Wane ne ya kare Shugaba Macron?
Wasu jami'an tsaro na musamman da ake kira GSPR ne suke bai wa shugabannin Faransa kariya.
An kafa su ne a shekarar 1983 kuma an ruwaito cewa tawagar ta mutum 77 ce da ta haɗa maza da mata da suke kare Mista Macron a lokacin taruka.
Wata tashar talabijin ta Faransa BFM ta ce jami'an na yin nazarin wurare kafin shugaban ƙasa ya ziyarta. Ana tura jami'ai masu ɗauke da makamai don su bai wa shugaban ƙasa kariya a lokacin da yake bulaguro.
Me mutane ke cewa?
Nan da nan 'yan siyasa suka yi tur da wannan mataki.
Firaiminista Jean Castex ya shaida wa Majalisar Dokoki jim kadan bayan hakan cewa ko da yake dimokradiyya tana nufin muhawara da samun sabani da ya kamata "amma bai kamata ya zama da tayar da hankali da zagi da kuma duka ba".
Shugaban jam'iyyar da ke da ra'ayin kwaminisanci Jean-Luc Mélenchon ya wallafa sakon Tuwita da ke "goyon bayan shugaban kasa".
Jami'ai sun bazama kan titunan Valence jim kaɗan bayan marin, a cewar wani saƙon Tuwita da wani ɗan jaridar Faransa ya wallafa.
Shugaba Macron yana wani zagaye ne a Faransa kuma ya kai ziyara wata makarantar hotron aikin otel ne a Tain-l'Hermitage.
Jami'ai sun ce an shirya cewa zai ci gaba da ziyarar tasa a ranar Talata, inda zai ziyarci wata cibiyar koyar da sana'o'i da aka kafa shekara 25 zuwa 30 da suka wuce.
Ziyarar shugaban ma zuwa ne a yammacin sassauta dokokin kullen annobar cutar korona da ƙasar ta yi inda za a buɗe wuraren cin abinci da mashayu bayan shaffe wata bakwai a rufe.