Sudan: Masu zanga-zanga sun buƙaci sojoji su yi juyin mulki

Protest in Sudan in favour of a military takeover, 16 October 2021

Asalin hoton, Getty Images

Masu adawa da yunƙurin dawo da tsarin dimokuraɗiyya a Sudan sun fito saman titunan Khartoum a ranar Asabar suna zanga-zangar neman sojoji su ƙwace ikon ƙasar.

Dubban masu zanga-zanga ne suka haɗa gangami a fadar shugaban ƙasa, yayin da rikicin siyasar ƙasar ke ƙara zafi.

Tun hamɓarar da shugaba Omar al-Bashir a 2019 ake mulkin karɓa-karɓa tsakanin Sojoji da fararen hula.

Amma fargabar rikici na ƙaruwa tun lokacin da aka yi yunƙurin juyin mulkin da aka hamɓarar wanda aka zargi magoya bayan tsohon shugaba Al Bashir a watan Satumba.

Tun lokacin shugabannin soji ke naman kawo sauyi na haɗaƙa tsakanin sojoji da kuma fararen hula da suka jagoranci zanga-zangar da ta yi sanadin kawo ƙarshen mulkin Al-Bashir a sudan.

Amma wani ɓangare na fararen hula na ganin buƙatar sojoji matakin ci gaba da mulki.

Farin jinin gwamnatin riƙon ƙwarya ya ragu sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Farin jinin gwamnatin riƙon ƙwarya ya ragu sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki

A ranar Asabar masu zanga-zanga sun ta yayata kalamai na adawa da gwamnati tare da yin kira ga shugaban sojin ƙasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya jagoranci juyin mulki domin kifar da gwamnati.

"Muna buƙatar gwamnatin soji, gwamnatin yanzu ta gaza tabbatar da adalci da daidaito," kamar yadda ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Saɓanin zanga-zangar da aka yi a ƙasar a baya, an ba masu zanga-zangar damar isa zuwa ga kofar shiga fadar shugaban ƙasa, kuma akwai ƙarancin ƴan sanda.

Masu goyon bayan gwamnati kuma sun kira zanga-zanga a ranar Alhamis domin adawa da zanga-zangar da masu adawa da gwamnati suka gudanar a ranar Asabar.

A ranar Juma'a, Firaministan Sudan Abdallah Hamdok, ya ƙaddamar da wani shiri na magance rikicin siyasar ƙasar wanda ya kira "mafi muni da hatsari" da aka gani a ƙasar cikin shekara biyu.

A watan Agustan 2019 aka rantsar da Mista Hamdok a matsayin Firaminista, bayan zanga-zangar da ta ba sojoji ƙwace mulki, matakin da ya kawo ƙarshen shugabancin Omar Al-Bashir na shekara 30.

Amma goyon bayan da gwamnatin riƙon ƙwarya ke samu ya ragu a watannin da suka gabata inda tattalin arzikin ƙasar ke taɓarɓarewa bayan cire tallafin mai da kuma tsadar farashin kayayyaki.