Shekaru biyu da hambarar da shugaban Sudan Omar al-Bashir

Masu zanga-zanga
Bayanan hoto, Mata sun taka muhimmiyar rawa a juyin-juya halin da Sudan ta fuskanta

A Sudan, ranar Laraba aka cika shekaru biyu da kaɗawar guguwar sauyin da ta hambarar da mulkin mulaka'un shugaba Omar al-Bashir na shekaru 30.

Rahotanni sun ce za a gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Khartoum.

Gwamnatin riko ta gabatar da tsauraran sauye-sauyen farfado da tattalin arzikin kasar, sannan ta yi nasarar samun farin jini daga kasashen waje.

A jiya Talata asusun bayar da lamuni na duniya IMF, ya amince da bai wa Sudan bashin dala biliyan biyu da rabi.

Sai dai tashin farashin kayayyaki, da janye tallafin mai ya sanya yawancin 'yan kasar cikin mawuyacin hali.

Ana kuma nuna damuwa kan dakarun da ke goyon bayan tsohuwar gwamnati na kokarin yi wa dimukradiyya zagon kasa.

Tun bayan hambarar da mulkin ne tsohon shugaban al-Bashir ke tsare hannun gwamnati mai mulkin Sudan.

Tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya bayyana gaban kotu a ranar 19 ga watan Agustan 2019, inda aka fara sauraren shari'ar da ake yi ma sa kan zargin cin hanci da rashawa a birnin Khartoum na kasar.

A watan Oktobar bara ne wata tawaga daga kotun kasa da kasa mai hukunta masu aikata manyan laifuka ta isa Sudan domin tattauna batun shari'ar tsohon shugaba Omar al-Bashir.

Kotun ta ICC na neman a mika ma ta al-Bashir domin ta hukunta shi kan tuhumar da ake ma sa da aikata laifukan kisan kiyashi da ya yi wa al'umomin kasar da laifukan yaki da kuma take hakkin bil Adama.

Gwamnatin ta Sudan kuma ta amince a gurfanar da shi a kotun kasa da kasa da ke birnin Hague.