Tsaro: Wasu jihohin arewa maso yamma a Najeriya za su ɗauki ƴan banga

Gwamnonin jihohin arewa maso yammaci da kuma tsakiyar Najeriya na niyyar ɗaukan ɗaruruwan ƴan bijilanti ko ƴan banga na musamman don taimaka wa jami'an tsaro a yaƙin da ake yi da ƴan fashin daji.

Yayin wani jawabi ranar Talata, Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya ce shi da takwarorinsa na Zamfara da Sokoto da Kebbi da Kaduna da Niger da kuma Nasarawa sun gana tare da amincewa da matakin ɗaukar 'yan bijilanti dubu uku don tunkarar 'yan fashin.

Waɗannan jihohin sun daɗe suna fama da matsalolin yan fashin daji da masu garkuwa da mutane don kuɗin fansa da dai sauransu.

Masanin harkokin tsaro a Najeriya Dokta Kabiru Adamu na ganin cewa wannan mataki ne mai muhimmanci kuma iya taimakawa wajen yaƙi da matsalar tsaron.

"Dama tsarin da muke da shi a Najeriya a halin yanzu a Najeriya bai wadatar ba, akwai giɓi a jihohi da kananan hukumomi, don haka matakin jihohin mai kyau ne," a cewar sa.

Ya ce wannan ɗaya ne kawai daga cikin matakan da gwamnonin suka ɗauka don haka idan aka haɗa da sauran matakan shawo kan matsalar ƴan bindiga da aka ƙaddamar a jihohin ana iya samun nasara a cewarsa.

Ya ce "Ya kamata gwamnatin tarayya da jihohin nan su bambance tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga da ake da su saboda sun rarrabu. Akwai waɗanda suke ɗauke da makamai don kare muradansu na dangane da rikici tsakanin manoma da makiyaya, a cikinsu kuma akwai ƴan bindiga da suka bijire wa doka kuma su nne masu cin zarafin ƴan ƙauyuka, sannan akwai masu satar mutane don kuɗin fansa."

Dokta Kabiru ya ce akwai yanayin da duka waɗan nan rarrabuwar ƴan bindiga za su saje da juna a gaza gane su.

"Don haka shawarar da za mu bayar shi ne tun da su ma ƴan bangar nan za su yi amfani ne da ƙarfi, ya kamata a yi ƙoƙarin ba su ingantaccen horo wanda zai taimaka wajen cikar burin kawar da ƴan bindigar nan," a cewarsa.

Ya ce tun da an taɓa ɗaukar irin wannan mataki a yankin arewa maso gabashin Najeriya, an ga kurakuran da aka yi, sai a gyara waɗannan kura-kuran.

Dokta Kabiru Adamu ya ce hanyar da ta fi dacewa ita ce amfani da ƴan bindigar wajen tattara bayanan sirri, da kuma gabatar da bayanan ga hukumomin tsaro na tarayya.

Ya ce ya kamata jihohi su ba su horon tattara bayanan sirri, sannan a kafa cibiyoyin tattara bayanan a kananan hukumomi da jihohi sannan jihohin sun kafa sansanonin haɗin guiwa a tsakanin jihohin inda za su riƙa tattara duka bayanansu.

"Idan ba a yi haka, wannan matakin ba zai yi wani tasiri ba. Sai an yi wa ƴan bangar horo mai tsauri yadda za su koyi ɗaukar bayanan sirri da isar da shi ba tare da wani ya sani ba," in ji shi.

Ƴan banga dai sun taka muhimmiyar rawa a yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya inda ake fama da rikicin Boko Haram.

Gwamnatin jihar Borno ta ɗauki ɗaruruwansu kuma ta ware masu albashi, inda suke aiki tare da jami'an tsaro wajen fatattakar mayaƙan Boko Haram.

Masana na ganin ƴan banga sun taimaka sosai wajen gano mayaƙan Boko Haram da daƙile hare-harensu da ƙwato garuruwan da suka ƙwace. Hak kuma, sun taimaka wurin tattara bayanan sirri da isar da su ga jami'an tsaro a jihar ta Borno.