Tsaro: Faransa ta janye jakadanta bayan Amurka ta harzuƙa ta

Faransa ta sanar da janye jakadunta da ke Amurka da kuma Australia zuwa gida a wani mataki na daban domin nuna bacin ranta a kan yarjejeniyar da Shugaba Biden na Amurka ya kulla domin Amurkar da Ingila su samar da jiragen ruwa na karkashin teku da ke amfani da makamashin nukiliya ga Australia a karkashin wata yarjejeniya ta tsaro ba tare da tuntubar jami'an Faransa ba.

Yarjejeniyar mai lakabin Aukus, za ta sa Faransa asarar kwangilar biliyoyin dala ta kera wa Australia jiragen ruwan na karkashin teku na gama-gari.

Ministan harkokin waje na Faransa , Jean Eve Le Drian, wanda ya sanar da matakin ya ce yi wa jakadun kiranye wani mataki ne na daban, wanda yanayi na daban ya janyo, kuma ya ce ya yi hakan ne a bisa umarnin shugaban kasar, Emmanuel Macron.

Shawarar Australia ta soke kwangilar da ta ba Faransa ta kera mata jiragen ruwa na karkashin teku na gama-gari, 12 kan dala biliyan 37, wadanda a maimakonsu ta koma ga Amurka domin sayen jiragen masu amfani da makamashin nukiliya ta shammaci Faransa, ta kuma harzuka ta.

Yawanci ana kallon yarjejeniyar, wadda Shugaba Biden da Firaministan Birtaniya Boris Johnson tare da takwaransa na Australia Scott Morrison suka sanar a ranar Laraba, a matsayin wani yunkuri na kalubalantar tasirin China a yankin tekun kudancin China.

China ta zargi kasashen uku da suka kulla yarjejeniyar da cewa suna da tunani ne na yakin cacar-baka.

Abin da ya kara bata wa jami'an Faransar ma rai shi ne cewa, sun ji labarin kwangilar ne kwatsam, 'yan sa'o'i kafin bayyana wa duniya.

Da kuma cewa wata sabuwar yarjejeniya ce ta tsaro da ta kunshi kasashe uku da suka hada da Birtaniya, wanda wannan ma wani abu ne na mamaki kacokan ga Faransar

Ministan harkokin wajen na Faransa ya bayyana kaduwa da mamaki a kan lamarin da ya kira yankan baya.

Manyan jami'an diflomasiyya na Faransa sun tattauna a game da rikici ko sabani mai nasaba ba da Australia kadai ba, har ma da Amurka, sannan kuma suka zargi Birtania da dabi'ar 'yan ta-fadi-gasassa, ko ci-ma-zaune.

Wani jami'in Amurka ya ce fadar gwamnatin kasar, White House ta yi nadama a kai, kuma ba ta ji dadin lamarin ba, da har ya kai Faransar janye jakadanta.

Jami'in ya ce kasarsa za ta tattauna da Faransar a kwanakin da ke tafe domin sasanta sabanin.

Ita ma da take Magana a Washington, Ministar Harkokin Waje ta Australia Marise Payne ta ce ta fahimci bacin ran Faransa, ta ce tana fatan aiki tare da kasar domin ta tabbatar ta fahimtar da ita muhimmancin da suke ba wa alakar da ke tsakaninsu.

Yarjejeniyar za ta sa a yanzu Australia ta zama kasa ta bakwai a duniya da ke amfani da jiragen ruwa na karkashin teku masu amfani da makamashin nukiliya.

Kuma a karkashin yarjejeniyar kasashen za su rika musayar fasahar intanet da kwamfuta da sauran wasu fasahohi na karkashin teku.