Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaban Faransa zai yaƙi aƙidar amfani da Musulunci wajen raba kan Faransawa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi alƙawarin karya lagon, a kan abin da ya kira matsalar yaɗa akidar amfani da Musulunci wajen raba kan al'ummar ƙasar.
A wani jawabi a wajen birnin Paris, ya ce wasu 'yan kalilan daga cikin Musulmin Faransa kimanin miliyan shida na da alamun gina wata al'umma kishiyar jamhuriyya ta Faransa, wadda ba a haDa ta da addini, don haka ya ce akwai buƙatar kafa tsauraran dokoki domin daƙile aikace-aikacensu.
A matakan da shugaban ya bayyana za a samar da doka da za a miƙa wa majalisar dokokin kasar, kafin ƙarshen wannan shekarar.
Daga cikin tanade-tanaden dokar, akwai tsattsauran sa ido da lura kan harkokin wasanni da sauran kungiyoyi, ta yadda ba za su zama wasu wurare ko dandali da masu tsattsaurar akida za su rika koyar da manufofinsu ba.
Sannan akwai kawo karshen tsarin aikawa da Limaman Musulunci zuwa Faransar daga wasu kasashe na waje, da sanya ido sosai a kan masallatai, ta yadda ba za su faɗa hannun masu tsattauran ra'ayi ba, da kuma kawo ƙarshen tsarin koyar da yara a gida.
Sai dai kuma ana ganin batun hana karantar da yara a gidan zai zama wani abu da zai jawo taƙaddama saboda yara wajen dubu hamsin da aka yi ƙiyasi ana koyar da su ba a makaranta ba a kasar ta Faransa, wato a gida a yau, yawancinsu ba su da wata alaƙa sam-sam da addinin Musulunci.
Jawabin na Shugaba Macron ya biyo bayan tattaunawa ce ta tsawon watanni da suka yi da shugabannin addinai da masana, kuma fadar gwamnatin ƙasar na nuna hakan a matsayin wata alama ta cewa shugaban na son yin magana a bayyane ba tare da wani shakku a kan hadarin tsattsaurar akidar Musulunci ba.
Sai dai 'yan kasar da dama na kallon jawabin a matsayin wata siyasa kawai, da shugaban ke gabatar da kansa a matsayin mai kishi ko kare kasar ta Faransa, ta wata hanya da zai kara kwantawa a ran masu zabe 'yan ra'ayin riƙau, sannan kuma ya kara farin jininsa domin zaben da ke tafe na shugaban kasa a shekara ta 2022.