Algeria: Tsohon shugaban ƙasar Abdelaziz Bouteflika ya rasu

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon Shugaban ƙasar Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika ya rasu bayan ya yi fama da doguwar jinya. Mista Bouteflika ya rasu ne yana da shekara 84.

Marigayin ya jagoranci Aljeriya na shekara 20 sai dai yunƙurin da tsohon shugaban ya yi na neman wa'adi na biyar ya jawo zanga-zanga kan titunan ƙasar.

Hakan ya sa shugaban ya yi murabus aka kuma kama wasu mataimakansa inda aka gurfanar da su gaban kotu bisa zargin cin hanci.

Mista Bouteflika ya taka muhimmiyar rawa wajen gwagwarmayar samun ƴancin Aljeriya a shekarun 1960 kuma an yabe shi matuƙa wajen kawo ƙarshen yaƙin basasan ƙasar da aka shafe shekaru ana yi.

Kafin ya zama shugaban ƙasar Aljeriya, sai da ya riƙe muƙamin ministan harkokin wajen ƙasar na shekara 16.