Korona: Italiya ta yi dokar tilasta ma'aikata nuna shedar rigakafi

Tuni daman aka yi dokar sa malamai da ma'aikatan makarantu su rika nuna takardar shedar ba sa dauke da cutar korona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tuni daman aka yi dokar sa malamai da ma'aikatan makarantu su rika nuna takardar shedar ba sa dauke da cutar korona

Italiya ta kasance kasa ta farko a Turai da ta yi dokar yi wa dukkanin ma'aikata su samu shedar yin rigakafin korona, ko shedar ba sa dauke da cutar ko kuma wadda ke nuna cewa sun warke daga koronar.

Dukkanin wanda ya saba wa dokar, wato ya yi burus da ita za a iya cin tararsa har yuro 1500.

Daga ranar 15 ga wata mai zuwa, Oktoba zai kasance dole ga ma'aikata kusan miliyan ashirin da uku (23) na gwamnatin Italiya da kuma na kamfanoni a kasar su gabatar da takardar shedarsu ta nuna cewa ba sa dauke da wannan cuta ta korona, da ake kira Green Pass, a duk lokacin da suka je wurin aiki.

Allurar rigakafin korona

Asalin hoton, Getty Images

Takardar za ta kasance dauke da bayanin da ke nuna cewa ma'aikacin ya yi akalla m rigakafin cutar ko da daya, ko gwajin da zai nuna ba ya dauke da ita ko kuma wanda zai nuna ya warke daga ita.

Duk wanda kuma bai nuna wannan sheda ba, za a iya dakatar da shi daga aikin ba tare da albashi ba kari kuma da tara mai yawan gaske.

Manufar wannan mataki dai ita ce domin ganin an shawo kan ma'aikata kusan miliyan hudu wadanda har zuwa yanzu ba su yi rigkafin cutar ta korona ba su yi.

Duk da 'yar zanga-zangar da wasu suka yi kan dokar, kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi ta nuna cewa da dama 'yan kasar ta Italiya sun amince da dokar.

Rigakafin korona

Asalin hoton, Getty Images

A matsayinta na kasa ta farko a yammacin duniya da annobar korona ta addaba, wadda kuma ta kasance ta biyu da aka fi samun mace-mace a sanadiyyar cutar, Italiyar ta yi kuskure wajen daukar matakai a duk tsawon lokacin annobar.

Shi ne a yanzu gwamnati take kokarin daukar mataki na dole na yin rigakafi ga dukkanin mutanen kasar.

Da yake sanar da dokar, Ministan Lafiya Roberto Speranza ya ce sabon matakin zai kare lafiyar jama'a tare da kara karfafa rigakafinsu.

Ya ce suna da kwarin gwiwa cewa matakin zai taimaka wajen bunkasa shirinsu na rigakafin.

Kusan kashi 65 cikin dari na yawan jama'ar kasar ta Italiya a yanzu an yi musu cikakken rigakafin, amma kuma ana samun karuwar masu dauke da cutar, abin da nau'in cutar na Delta ke haddasawa.

Allurar rigakafin korona

Asalin hoton, Others

Italiya ta samu mutane sama da miliyan hudu da dubu 600 da suka kamu da cutar ta korona, mutane 130,000 suka rasu a sanadiyyar cutukan da ke da nasaba da ita tun bayan bayyanar barkewar annobar bisa bayanan Jami'ar Johns Hopkins

Da farko an bullo da wannan takardar shed ace ta korona domin inganta tafiye-tafiye a cikin kasashen kungiyar Tarayyar Turai.

Kuma tun daga sannan kasashe da dama suka bullo da tsarin gabatar da takardar a bisa dalilai daban-daban.

Faransa ta bullo da nata domin shiga kantuna da wuraren cin abinci, da mashaya da shiga jirgin sama da jirgin kasa, kamar yadda suma kasashen Austria da Cyprus da wasu kasashen na Turai suma suka bullo da irin tsarin.