Wani mutum ya boye gawar mahaifiyarsa a rumbun giya har shekara daya don karbar fanshonta

An Austrian police officer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa

Wani mutum ya boye gawar mahaifiyarsa a wani daki da ke kasan gidansa fiye da shekara daya yana karbar fanshonta, a cewae 'yan sandan kasar Austria.

Ana tsammanin matar mai shekara 89, ta rasu ne sakamakon cutar mantuwa da ta yi fama da ita a watan Yunin bara.

An ce dan nata mai shekara 66 ya sanya gawar tata ne a rumbun da yake ajiye giya ya jibga kankara a kan gawar don hana ta wari.

'Yan sanda sun yi amannar cewa ya karbi kusan fan miliyan 42,000 ba bisa ka'ida ba a cikin kudin fanshon nata.

An gano lamarin zambar ne bayan da wani mai kai sakon takardu ya ce an hana shi ganin matar a lokacin da ya bukaci hakan, a cewar sanarwar 'yan sanda.

Hakan ne ya jawo aka fara bincike ya kuma sa aka gano abin da mutumin ya aikata.

'Yan sanda sun shaida wa kafar yada labaran Austria ta ORF cewa mutumin ya kuma lullube mahaifiyar tasa da kashin mage. "An adana gawar ne," in ji dan sanda Helmuth Gufler, yana mai cewa mutumin ya amsa laifinsa.

Mr Gufler ya ce mutumin ba shi da hanyar samun kudade, sannan ya ce musu ya san za a daina biyan fanshon nata ne da zarar ya sanar da mutuwarta, wanda hakan zai sa ya kasa biyan kudin jana'izar mahaifyar tasa kuma zai iya rasa gidan da suka zaune a ciki.

Ya kuma ya gaya wa dan uwansa cewa mahaifiyar tasu tana asibiti ana kula da ita, sannan bai kamata a xiyarce ta ba saboda a halin da take ciki ba ta gane kowa, kamar yadda kafar ORF ta ruwaito.