Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan 'tsadar gas'

...

Asalin hoton, Getty Images

Da alama ƙarin da da aka samu gutsin-gutsin na gas ɗin girki a Najeriya ya sa ƴan ƙasar shiga wani hali, ganin yadda gas ɗin ya yi tashin gwauron zabi cikin ƙasa da watanni takwas.

Tukunyar gas mai nauyin kilo 12.5 da ake sayarwa a kan 3,500 a Disambar 2020, a yanzu ana sayar da ita a kan 6,800 a wasu sassan Abuja.

Wasu mazauna Legas kuma na cewa suna sayen gas ɗin a kan naira 7,200, kuma akwai hasashen zai iya kai wa naira 10,000 zuwa Disambar wannan shekara.

Wannan yanayi da ake ciki masana na cewa zai sake haifar da matsi musamman tsakanin marasa arfi da ke kukan tsadar rayuwa a kullum.

Baya ga haka a makon nan ne ake iƙirarin cewa za a yi ƙarin kudin wuta a Najeriya, duk da mahukunta a ɓangaren na cewa duk jita-jita ce ake yi kan batun.

Me masana tattalin arziƙi ke cewa?

Dangane da wannan batu, BBC ta tuntuɓi Muhammad Auwwal Mahmud, wani mai sharhi kan tattalin arziki a Najeriya inda ya ce matsalolin da ake da su a Najeriya sun wuce duk inda ake tunani.

A cewarsa, ƙarin farashin gas da duk wani makamashi da ake amfani da shi a Najeriya na da tasiri matuƙa ga tattalin arzƙin ƙasar.

"Lokacin da aka kai tattalin arziki bango kuma ana danna masa kaya, kamar a ce jaki ne a ɗora masa kaya masu yawa kuma a ce ana ƙoƙarin dora masa wasu kayayyaki, abin da ake ƙoƙarin ɗora masa ko dai ya kashe shi ko kuma ya nakasa shi," in ji Auwwal Mahmud.

A cewarsa, dalilin da ya sa aka ƙirƙiri amfani da shi kansa wannan gas ɗin shi ne domin rage ɗumamar yanayi, ganin yadda ake amfani da itace da sauran makamashi masu samar da hayaƙi da ke gurɓata muhalli.

..

Asalin hoton, Getty Images

Ya bayyana cewa ganin yadda jama'a da dama a Najeriya suka koma amfani da wannan gas ɗin domin girki, ya zama cewa ƙasar ba ta iya samar da adadin gas din da ake buƙata wanda hakan ya sa ake shigo da wani kaso na gas ɗin cikin ƙasar.

"Babbar matsalarmu a Najeriya ita ce matatun da muke da su ba sa aiki yadda ya kamata don su samar da gas ɗin a gida," in ji shi.

Ya ce da a ce Najeriya na samar da gas din da take amfani da shi kashi ɗari bisa ɗari, da tana da ikon ta yanke hukunci kan duk irin farashin da take so ta saka wa gas ɗin.

Amma ganin cewa ana sayen wani kaso daga gas din da ake amfani da shi a cikin ƙasar, dole sai farashin da ake amfani da shi wurin sayo shi a kasuwannin duniya ya yi tasiri ga farashin da ake sayar da shi a Najeriya.

Me ƴan Najeriya ke cewa kan ƙarin kuɗin gas?

Ƴan Najeriya da dama na ƙorafi a shafukan sada zumunta kan ƙarin kuɗin Gas. A makon da ya gabata, BBC ta tambayi ƴan ƙasar nawa ake sayar da gas ɗin girki a inda suke.

Jama'a sun ta bayar da amsoshi daban-daban inda har aka samu wani mai suna Booster Boy da ke zaune a Legas da ya ce ya sayi Gas a kan naira dubu bakwai, ƙaramar tukunya mai ɗaukar kilogram 12

.

Yasir Ramadan Gwale kuma ƙorafi ya yi a kan yadda ya ga ana siyar da tukunyar gas kan naira 6000 duk da cewa Najeriya na da arziƙin gas.

.

Shi kuma Sultan Abdullahi cewa ya yi an cika masa tukunyar gas dinsa kan naira dubu shida, abin da a baya aka saba yi masa kan 4,150.

..

Ummu Tau'am kuma ta ce an tashi daga amfani da kalanzir an koma amfani da gas, wanda hakan ya sa take tunanin nan gaba ko da me za a koma amfani?

.