Tsakanin gawayi, kalanzir da iskar gas wanne ya fi sauƙi?

Gidajen mai sun rage saidawa abokan hulda da ke siyan kalanzir a galan-galan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mace na jiran layi ya zo kan ta a gidan mai

A Najeriya, tsadar makamashin girki na kalanzir ta addabi jama'a bayan da farashinsa ya yi tashin gwauron-zabi, inda bayanai suka nuna farashin galan ɗaya ya kai naira 1,200.

Galibi talakawa wadanda su ne suka fi yawa, na dogara da kalanzir wajen amfanin yau da kullum na girke-girke, wanda kuma ƙarancinsa kan tilasta wa wasu amfani da itatce, ko gawayin kwal da kuma iskar gas.

Farashin tukunyar gas babba yakan kai naira 5,000 da wani abu, a yayin da tsaka-tsaki kuma kan kai 3,000. Sai kuma na kasa da hakan da akan samu kan 2,000. Kazalika akwai kuma ta 1,000 - duka ya danganta da girman tukunyar.

Tukunyar gas na girki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu wuraren ɗura gas kan ɗura wa mutane gas ɗin daidai da aljihunsu

Sai dai galibi gidajen sayar da gas na girki kan ɗura wa mutane daidai aljihunsu, musamman masu kananan tukwanen.

Shi kuwa gawayin girkin kamar yadda wata mace ta shaida wa BBC, ana sayar da kwano ɗaya kan naira 90 zuwa 100, sannan buhunsa kan kama daga naira 1,800. Akwai na 2,500 har zuwa 6,500 - ya danganci girman buhun da kuma yawan kwanon da yake ci na gawayin.

Galibin waɗanda BBC ta tattauna da su sun bayyana cewa yanzu sun daina amfani da kalanzir tun tuni saboda tsadarsa, suna masu cewa sauran hanyoyin samar da makamashin girki irin su gas da gawayi da kuma itace sun fi sauƙi idan aka kwatanta da kalanzir din wanda kudinsa ya haura yadda suka saba saya.

Unguwannin da ba su da gidajen mai, sun dogara ne da 'yan kasuwar da suka saro kalanzir domin bukatun yau da kullum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ɗan bumburutu (mai sayar da mai a kasuwar bayan fage)

Wata da ke amfani da kalanzir mazauniyar unguwar Hotoro a Kanon Najeriya, ta shaida wa BBC cewa ba a cika samun sa a gidajen mai ba yanzu.

"Yawanci kafin mu je mu saya sun sayar wa 'yan sari, don haka da wuya ka je gidajen mai ka samu layin masu sayan kalanzir," in ji Hadiza Muhammad. "Dole ta sanya muke siya a hannun 'yan kasuwar bayan fage, wadanda su ma sukan ce 'yan sari ne ke sayar musu.

"Ko a Lahadin ƙarshen mako na sayi galan ɗin kalanzir mai cin lita huɗu kan N1,200. Akwai waɗanda ma suke sayarwa kan N1,300, amma ina samun sa da sauƙi saboda mun saba da wanda na ke saya a wajensa.''

Farashin buhun gawayin girki da kuma gas na manyan tukwane kan kai sama da N5,000, yayin da kanana da matsakaita na tafi-da-gidan-ka kan kama daga N2,000 zuwa NN3,000. A wasu lokutan, a gidajen sayar da gas ɗin mutane kan samu a ɗura musu daidai aljihunsu.

Malama Fatima Haruna da ke unguwar 'Yan kaba ta Jihar Kano ta ce ta shafe shekaru tana amfani da kalanzir wajen dafa abinci, amma yanzu ta sauya zuwa amfani da wasu makamashin girki saboda tsadarsa.

''Ai yanzu amfani da kalanzir akwai matsala, ga tsada ga kuma jinkiri kafin abincin ya nuna, amma gawayi kwano ɗaya na N100 zai ishe ka dafa abincin safe zuwa dare, kuma ba shi da matsala da zarar wutar ta ruru,''a cewar malamar.

Ta ƙara da cewa kwanan nan ta fara amfani da madaidaiciyar tukunyar iskar gas wajen dafa abinci, wanda takan rika sauyawa lokaci zuwa lokaci da gawayin, wanda ta ce hakan ya fi sauki a gare ta.

''Kin ga ana ɗura min gas ɗin a kan N2,000 ne, wanda yana kai ni tsawon wata ɗaya bai kare ba, kuma a wasu lokutan ma a kan dura maka gas din daidai kudinka ne. Gas yana biya min bukata wajen kammala girki cikin sauri, ba kamar kalanzir ba, kuma idan aka kwatanta komai tsadarsa gas din ya fi, saboda akwai biyan bukata''.

Malama Hajara Ibrahim kuwa da ba ta da karfin sayen gas din, ta shaida wa BBC cewa gawayi ko kuma itace take amfani da shi a maimakon kalanzir saboda yanzu ya fi karfin aljuhunta.

''Idan na sayi kwanon gawayi na N100, ko kuma ɗaurin itace mai guda biyar zuwa shida na N50 ko N100, sukan jima ina dafe-dafen abincina,'' in ji ta.

Masana na bayyana illolin da rashin itatuwa ke haddasawa kamar sauyin yanayi da dumamarsa, abin da kuma ƙasashen duniya ke yaƙi da shi.

Tsadar kalanzir ba kawai magidanta ko kuma ma'aurata take shafa ba, har ma ma da masu sana'ar da ta shafi amfani da shi, kamar yadda wani mai sayar da shayi da taliyar Indomie Malam Sanusi Bukar ya bayyana.

Ana zargin 'yan bunburutu da kara farashin kalanzir
Bayanan hoto, Teburin 'yan bumburutu

''Kin ga idan zan dafa wa kostomomina Indomie da soyayyen ƙwai, dole in yi amfani da rusho in zuba kalanzir, amma nakan yi amfani da itace wajen dafa shayin, dole tsadar kalanzir ta daga min hankali,'' in ji Sanusi mai shayi.

Malama Aisha Anto mai waina kuwa, ta ce amfanin kalanzir ba shi da yawa a banagaren sana'arta, don takan yi amfani da murhun gargajiya ne wanda itace kawai yake bukata, kuma ma takan yi amfani da ledoji wajen hura itacen girkin, sabanin yadda a da akan dan watsa kalaznir.

''Na kan sayi damin itace da yawa daga dillalai da kan yi yawo da su a cikin motocin a-kori-kura suna sayarwa, kuma yana yi min auki sosai. Na san in da a ce kalanzir ne ba zan fita ba ballantana in samu riba a sana'ata."

'Yan Najeriya na fama da matsalar tsadar kalanzir saboda karancinsa a kasar mai arzikin fetir, inda a yanzu ake sayar da lita ɗaya kan kusan N400 a gidajen sayar da mai.

A kasuwannin bayan fage kuma farashin ya zarce haka, al'amarin da ya jefa jama'a cikin mawuyacin hali lura da yadda suke dogaro da kalanzir a matsayin makamashin girki.

Me ya sa farashin kalanzir ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya?

Wasu mutane a kan layin sayen fetur a Jihar Legas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan kasuwa sun ce ƙarancin dala a kasuwar canji na ƙara ta'azzara tsadar kalanzir

Alhaji Bashir Dan Malam, shugaban masu dakon man fetur da dangoginsu ne a Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa dole ce ta sanya farashin kalanzir din ya tashi, sakamakon cire tallafin da gwamnati ta yi a kan man fetur da dangoginsa.

"Yan kasuwa ne ke zuwa kasuwar bayan fage su samu dalar Amurka da za su sayi kayan nan da su, sannan farashin kan sauya, ba lallai yadda ka samu dala a yau ya kasance haka take a gobe ba, akan samu sauyi," in ji Dan Malam.

"Don haka dan kasuwa da ya sayi dala da tsada ya kuma saro kalanzir ko man fetur ko gas daga kasar waje, dole ya ci riba komai kankantarta, tun da harkar duka ana yi ne domin riba.

"Kuma a yanzu kowa ya san cewa farashin man fetur ya kara tashi a kasuwannin duniya, rashin tabbas din farashin dalar Amurka ya kara taka muhimmiyar rawa wajen karuwar farshain kalanzir.''

Mutane da dama na ƙorafin cewa yawancin gidajen mai sun daina sayar musu kalanzir, abin da ya sa suke samun sa da matukar tsada a hannun 'yan sari saboda su ma kasawa suke yi sannan su ci riba. Bashir Dan Malam ya ce wannan kuma yana da alaka da kokarin da suke yi na sayen kaya a dunkule yadda za su kara saro wasu cikin gaggawa.

''Misali idan a baya kana saro kalanzir kan miliyan 10, yanzu ya zama miliyan 15 har zuwa 20, sannan ka zo ka ajiye ana sayen sa da galan-galan ko kadan-kadan, don haka ana daukar dogon lokaci kafin su gama sayarwa.

"Batun sarrafa wutar lantarki ko man dizel da ake amfani da shi a injinan da ake sayar da kalanzir din suna cin kudi ba kadan ba, kuma ta nan ribar ke zurarewa.

"Don haka sun gwammace su sayar wa 'yan sari. Ana kuma kai su kauyuka ko wuraren da mota ba ta shiga. Ko a jihar Kano akwai wuraren da ba su da gidajen mai kamar unguwar Yakasai, don haka dole ne sai an rarraba wannan kaya ta yadda mazauna yankin za su samu saya a saukake.''

Sai dai ya kara da cewa, ba dukkan gidajen mai ne suke sayar wa 'yan kasuwa sarin kalanzir ba, akwai gidajen mai da dama da har yanzu suke sayar da kalanzir, sai dai farashin ya danganta da yadda dan kasuwa ya samu dalar Amurka.

Hakan na nufin babu wani tsayayyen farashi a hukumance kan yadda za su sayar shi.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin hukumar da lamarin ya shafa, sai dai ba mu iya cimma hakana ba.

Tsadar rayuwa na kara zama wani babban kalubale ga talakawa 'yan Najeriya. Baya ga tsadar da iskar gas da kalanzir da man fetur ke yi, farashin kayan abinci ma ya yi tashin da aka dade ba a gani ba lamarin da ke kara tsunduma 'yan kasar cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi.