Hisbah: Abin da ya sa rundunar ke neman tauraruwar Kannywood Ummah Shehu

Asalin hoton, Facebook/Ummah Shehu
Hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce tana gayyatar tauraruwar fina-finan Kannywood, Ummah Shehu, domin ta yi mata karin bayani bisa zargin da ta yi wa wasu jami'anta.
Babban Kwamandan rundunar, Harun Sani Ibn Sina, ya shaida wa BBC Hausa suna neman tauraruwar ne bayan da ta yi zargin cewa jami'an Hisbah suna aikata laifuka amma sun ki duba nasu suna takurawa talakawa marasa galihu.
Wasu rahotanni sun ambato tauraruwar tana yin raddi ga hukumar Hisbah bayan da ta kama kama wata ƴar wasan Kannywood da kuma ta yi fice a kafar sada zumunta, Sadiya Haruna, kan "yaɗa hotunan batsa" a shafukanta na sada zumunta.
Rahotannin sun nuna cewa Ummah Shehu ta fusata matuka kan matakin da Hisbah ta dauka inda ta yi zargin cewa hukumar ta fi mayar da hankali wajen hukunta talakawa da 'yan fim bayan kuwa masu hannu da shuni da kuma jami'an hukumar suna tafka ta'asa ba tare da an yi musu hukunci ba.
Sai dai mun yi yunkurin jin karin bayani daga gare ta amma ba ta amsa kiran wayar da muka yi mata ba.
Amma Babban Kwamandan rundunar, Ibn Sina, ya ce suna neman Umma Shehu domin ta yi musu bayani dalla-dalla kan zarge-zargen da ta yi musu.
A cewarsa, idan ba ta je ta yi musu bayani kan batun ba za su kai kararta a gaban kotu inda za su tuhume ta da laifin yi wa Hisbah kazafi.
Ibn Sina ya ce "ba wai muna nemanta ruwa a jallo ba ne; abin da muke cewa shi ne ta zo ta yi mana karin bayani kan zarge-zargen da ta yi mana domin kowa ya sani.
"Idan abubuwan da ta fada na bukatar bincike za mu bincika, idan kuma ta kasa gamsar da mu, to za mu kai ta kotu domin zargin yi mana kazafi."
'Yan Najeriya da dama dai suna zargin hukumar ta Hisbah da mayar da hankali kan marasa karfi sanna ta bar masu mulki ko masu kudi a kan batun aikata laifi.
Ko a farkon watan da muke ciki, hukumar ta Hisbah ba ta dauki mataki kan wasu hotunan 'yar Sarkin Bichi, Zarah Nasiru Ado Bayero ba, wadda ɗan shugaban ƙasa Yusuf Buhari ya aura, bayan da aka rika yaɗa hotunanta sanye da wata doguwar riga mai shara-shara.

Asalin hoton, Other
A cikin hotunan waɗanda ba a gan ta tare da angon ba, babu ɗan kwali a kan gimbiyar ta Masarautar Bichi da ke Kano sannan kuma saman rigar yana da launin fatar jikinta.
Kwamandan Hisbah Harun Muhammad Ibn-Sina ya ce aikin hukumar shi ne hana yaɗa ɓarna ko da kuwa ta faru a baya, ba wai "tonowa da kuma hukunta mutum ba".











