Amurka na shan matsin-lamba kan ficewa daga Afghanistan

Asalin hoton, AFP
Amurka ta ce tana magana da Taliban a game da yadda za a iya iko da filin jirgin saman Kabul a nan gaba, yayin da gwamnatin Shugaba Joe Biden ta ce za ta yanke shawara cikin sa'o'i 24 kan ko za ta kara wa'adin ficewa daga Afghanistan na raanar 31 ga watan nan na Agusta.
Gwamnatin Amurka ta ce tana tuntubar Taliban kusan a kullum.
Daya daga cikin batutuwan da suka taso har Amurkar ta fadi hakan shi ne na wane ne ke iko da filin jirgin saman babban birnin Afghanistan, Kabul, inda dubban mutane suka yi cuncurundo a wajensa, da zummar son ficewa daga kasar tun bayan da 'yan Taliban suka kwace gwamnati.

Asalin hoton, Reuters
Kakakin Ma'aikatar harkokin Wajen Amurka, Ned Price ya ce, akwai yarjejeniya tsakanin Amurka da kawayenta da kuma Taliban kan cewa lalle akwai bukatar a samu filin jirgin sama da yake aiki- kuma a yanzu Amurkar ta dogara ne ga kungiyar ta Taliban mai tsattsauran ra'ayi wajen tabbatar da tsaro a filin jirgin.
A halin da ake ciki kuma an ce ana samun sabanin ra'ayi da abin ya kai ga jayayya a tsakanin masu ba Shugaba Biden na Amurka sha'awara a kan kara wa'adin ficewa daga kasar har bayan ranar 31 ga watan Agusta bisa dalilai na tsaro.
A bisa yarjejeniyar da aka yi da Taliban dole ne Amurka ta fice daga kasar zuwa ranar 31 ga watan nan na Agusta.
Amma kuma Faransa da Burtaniya da Jamus dukkaninsu suna nuna cewa akwai bukatar kara lokacin ficewar yayin da ake shirin gudanar da taron shugabannin kungiyar kasashe bakwai mafiya karfin tattalin arziki, G7 a yau Talata.

Asalin hoton, UNKNOWN
Cikin sa'o'i 24 ne nan gaba a yau din ake sa ran Shugaba Biden zai yanke shawara a game da batun a yayin taron na kasashen G7, kamar yadda wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Sai dai kuma Taliban tuni ta mayar da martani inda ta sheda wa BBC cewa duk wani karin wa'adi zai zama saba yarjejeniyar da aka yi, tana mai gargadi da cewa akwai abin da zai biyo bayan ci gaba da kasancewar dakarun wajen a kasar.
Dubban mutane aka kwashe daga babban birnin kasar ta Afghanistan ,Kabul, amma kuma har yanzu akwai wasu dubban da ke cunkushe a ciki ko kuma kusa da filin jirgin saman birnin wanda dakarun Amurka da kawayenta ke kula da tsaronsa.
Da yawa daga cikin mutanen da ke tserewa daga kasar, musamman ma wadanda suka yi aiki da sojojin kasashen waje, suna jin tsoron ramuwar gayya ne daga 'yan Taliban, wadda ta sanya tsauraran dokoki lokain tana rike da mulki daga 1996 zuwa 2001.
Mutane suna nuna fargaba ne duk kuwa da cewa 'yan Taliban sun nemi kwantar musu da hankali, inda suka ce wadanda suka tsaya za su taimaka wajen sake gina kasar.

Asalin hoton, EPA
Kakakin Taliban din Suhail Shaheen ya sheda wa BBC cewa mutanen da suke da fasfo za su iya barin kasar a jiragen kasuwa ko da kuwa bayan wa'adin ficewar dakaraun na waje ne, ya ce amma in so samu ne, suna son su tsaya a kasar, amma duk wanda yake son ficewa, na iya ficewa.
An fara kwashe mutane ne daga kasar yayin da Taliban ta kama Kabul, a mamayar da ta yi wa kasar bayan matakin Amurka na janye sojojinta daga kasar.
Kusan dan yankin da ya rage da ba ya hannun Taliban din shi ne na
Panjshir da ke arewa masu kudu da Kabul, inda tunga ce ta masu kin jinin Taliban, wadanda suka ce dubban mutanen da ke can a shirye suke su ci gaba da yaki da Taliban











