Ibrahim Mantu: Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya ya rasu

Asalin hoton, Getty Images
Allah Ya yi wa tsohon mataimakin shugaban Majalisar dattijan Najeriya Ibrahim Mantu, rasuwa.
Wata majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar wa BBC cewa Sanata Mantu ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Majiyar ta ce ya rasu a wani asibiti a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, bayan ya shafe kwana 10 a kwance.
Za a yi jana'izarsa da misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Talata a Masallacin Sheikh Imam Nuru Khalida da ke Rukunun gidajen 'yan majalisar dokoki da ke Apo.
Sanata Mantu ya yi suna sosai a lokacin da yake mataimakin shugaban majalisar dattijai daga tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007.
Sanata Mantu a taƙaice
An haifi Sanata Ibrahim Nasiru Mantu a shekarar 1947 a jihar Filato da ke yankin tsakiyar Najeriya.
Ya yi karatunsa da Najeriya da kuma Birtaniya.
Ya fara shiga harkokin siyasa tun a shekarar 1978, sannan a 1993 ya zaman darakta janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar National Republican Convention-NRC.
Sannan ya yi kakakin jam'iyyar United Nigeria Congress Party- UNCP.
Ya zama sanata a shekarar 1999 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP mai mulki a wancan lokacin, sannan ya zama mataimakin shugaban majalisar dattijai daga shekarar 2003 zuwa 2007.











