WhatsApp ya ɓullo da sabon tsarin ɓacewar hotuna da bidiyo

WhatsApp ya ce tsarin zai zama tamkar kariya ga masu amfani da manhajar, musamman wajen aikawa da lambobin sirri ko hoton da ba a bukatar ddewrsa

Asalin hoton, WhatsApp

Manhajar WhatsApp ya ɓullo da sabon tsarin da zai bai wa masu amfani da shafin damar ɓatar da hotuna da bidiyon da aka aiko musu bayan dan wani lokaci.

Bayan wanda aka aikawa hoton ko bidiyon ya bude su a karon farko, za su ''kalla sau daya'', daga nan sai ya goge da kan shi ba tare da ya fada ma'ajiyar hotuna da ke cikin wayarsa ba.

WhatsApp ya ce an dauki matakin ne domin bai wa masu amfani da shi karin damar sarrafa shi yadda suke bukata, da samun karin kariya.

Sai dai, masu kare hakkin yara su na nuna damuwa kan bacewar hotunan ko sakwannin ko da kuwa mutum bai bukaci hakan ba, zai taimaka kan boye wata shaida musamman idan an ci zarafin yara ta hanyar lalata.

Dama dai ana takun saka tsakanin hukumar yaki da cin zarafin kananan yara ta kasa da kasa da uwar manhajar WhatsApp, wato Facebook kan amfani da sakon sirri.

Irin wadannan sakonnin na sirri, na nufin jami'an tsaro, ko 'yan sanda ba za su ga sakon da aka aikawa mutum ba, sai wanda aka aikewa da wanda ya aiko ne kadai za su gani.

Amma tsarin goge sako na kai tsaye na nufin idan jami'an tsaro suka kwace wayar wanda ake zargi da aikata laifi babu abin da za su gani cikin sakwannin da aka aiko ma sa ko ya aika.

"Tsarin goge hotuna ko bidiyo na kai tsaye, ka iya sanya rayuwar yara cikin babban hatsari fiye da lokutan baya.

"Musamman idan an ci zarafinsu, ko ana neman wata shaida da ta shafi cin zarafi ta hanyar lalata da su," in ji Alison Trew, jami'in gidauniyar ba da kariya ta shafin internet.

Sai dai shi WhatsApp na kokarin tallata hajar ne ga abokan hulda na kud-da-kud, tare da kare matakin da cewa zai yi amfani idan mutum baya bukatar hotunan.

Misali idan mutum ya je sayan kya a wani shago sai ya gwada riga ko wando, to hotunan da ya aika domin taya hi zabe ba su dauki dogon lokacin da za su zama hadari ba tun da bacewa za su yi, ko aikawa wani lambobin ka na sirri.

Ma'adanar ajiye hotuna

"Ba kowanne sako ko hoto da muka aika ne muke so ya kasance cikin hotunan da ke cikin akwatin adanawa da ke wayoyinmu ba" in ji WhatsApp.

"Yawancin wayoyi ,daukar hotuna da adanasu na cushe ma'adanar ajiye hotunan."

Kuma za a fara amfani d wannan sabon tsarin na bacewar hotuna "kuma kowa zai fara fuskantar hakan a cikin makon nan".

Masu amfani da manhajar za su gane idan an kalli hoto ko bidiyon sau daya, saboda abin da ke nuna an gani ba lallai ya nuna ba, sai dai wata babbar alama ta "1" za ta nuna maimakon abin da muka saba gani a baya.

Kamar dai yadda sakwanni da hotuna ko bidiyo da wanda aka wallafa da wanda ba a wallafa ba suke bacewa a manhajoji kamar other apps such as Snapchat, matukar ba mu yi gaggawar adana shi ba, to shi ma haka sabon tsarin na WhatsApp zai kasance.

Sai dai mau amfani da manhajar ko wanda aka aikewa sakon zai yi saurin kwafar shi, ko saurin nadar muryar da zarar an bude, ko kuma daukar hoton allon wayar ko bidiyo da wata wayar ta daban, shi ne kadai hanyar da za a iya samun wannan abun da ya goge.

Sai dai tsarin zai zo da wasu tsare-tsare da ƙa'idoji:

  • Ba za a iya adana hoton a ma'adanar hotuna ko manhajar da ke kan waya ba
  • Ba za a iya aikawa wani hoto ko bidiyon ba, ko adanawa
  • Matukar suka haura makonni biyu, amfaninsu ya kare

Ana goge duk wasu sakwannin rubutu na wanda ya aika da wanda aka aikawa bayan mako guda, wannan shi ne daya daga cikin damuwar da gwamnatin Birtaniya ta nuna.

Dokokin Birtaniya, sun ce duk wasu bayanai da suka shafi wata tattaunawa ko mataki, ana bukatar adanawa saboda idan baukatar su ta taso ka san inda za ka samu.

Yawancin jami'an gwamnatoci na amfani da manhajar WhatsApp ko makamantansu akai-akai, lamarin da ya sa wata kungiya ke gangamin ya kamata a tuhumi jami'an gwamnati da ke aikawa da sakwannin.

Sai dai 'yan majalisa sun ce ana daukar matakan da suka dace, domin tabbatar sakwannin da jami'an gwamnati ke aikawa juna ba su sabawa doka ba.