Miyetti Allah ta yi alƙawarin tona asirin masu satar mutane a Taraba

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin Fulani makiyaya a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya sun yi alƙawarin tona asirin duk wani da suka gano mai aikata laifi ne daga cikinsu.
Ƙungiyar Miyetti Allah reshen Taraba ce ta ɗauki wannan matakin tsakanin mambobinta da suka ƙunshi shugabanin Fulani makiyaya da ardo-ardo a fadar Sarkin Muri Alhaji Abbas Tafida.
Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na jihar Taraba Alhaji Sahabi Mahmud Tukur ya shaida wa BBC cewa wa'adin wata biyar ƙungiyar ta ba kanta domin kakkaɓe ɓata-garin da ke ɓata sunan Fulani makiyaya.
"Idan akwai ɓatattu cikinmu za mu kira su mu tattauna da su mu nuna musu gaskiya idan kuma suka ƙi za mu miƙa su ga hukuma."
"Idan an ce ba mu da kyau, to za mu duba domin mu gano su don mu gyara wankanmu ko da kuwa ƴaƴanmu ne," in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan aikin da suka yi alƙawali ya zama wajibi domin wanke sunan Fulani daga ɓata sunan da ake masu na fashi da makami da satar mutane.
Shugaban na Miyetti Allah a Taraba ya yi iƙirarin cewa ba Fulani ba ne kawai ke aikata laifin fashi da makami da satar mutane ba - "amma an fi fakewa da Fulani shi ya sa muka yanke shawarar shiga cikinmu mu fito da duk wani mai aikata laifi domin wanke zargin da ake muna."
Miyetti Allah ta ce za yi amfani da ƴan banganta a sassan Taraba da ke kula da rumfunan Fulani domin tantance ɓata-gari daga cikinta domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Sai dai ƙungiyar makiyayan ta bayyana damuwa kan yadda jami'an tsaro ke kama ƴaƴan Fulani da ba su ji ba su gani ba.
Alhaji Sahabi Mahmud Tukur ya buƙaci sarkin Muri ya gabatar da korafinsu ga gwamna Darius Ishaku kan yadda ake kama Fulani ba tare da tabbatar da zargin da ake masu ba inda ya buƙaci gwamnati ta saki wadanda aka tabbatar da ba su da laifi.
A lokacin bikin Babbar Sallah ne Sarkin Muri, Abbas Tafida, ya bai wa Fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 na su bar dazukan jihar ko kuma su daina garkuwa da mutane.
Kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce tsakanin al'umma da makiyaya.











