'Ina gani aka rutsa dana mai shekara biyu da bindiga'

Hadiza Hashim
Bayanan hoto, Cikin yanayin rashin samun taimako Hadiza Hashim tana kallo masu garkuwa da mutane suka dauke ɗan karamin ɗanta
    • Marubuci, Naomi Scherbel-Ball
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos

Sama da yara 300 da aka sace a makarantu a Najeriya har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane, da yawa ba a ji ɗuriyarsu ba kusan watanni biyu ke nan, wasu daga cikinsu ba su fi shekara biyu da haihuwa ba.

An kuma saki sama da yara 1,000 da aka sata, wadanda ake karbar kudaden fansa akai-akai daga hannun iyayensu, ɗaruruwan iyalai har yanzu suna jiran labarin halin da 'ya'yansu ke ciki.

BBC ta tattauna da iyaye da yawa game da satar 'ya'yansu da kuma tunanin yadda za su ci gaba da barin 'ya'yansu zuwa makaranta lokacin da ake tsaka da wannan balahira.

Short presentational grey line

'Ba 'ya'yan kowa ba ne su'

Hadiza Hashim na da yara biyar ta je bakin makarantar Islamiyyar da ke Tagina a jihar Neja, ranar 30 ga watan Mayu lokacin da aka sace ɗaliban makarantar 134.

Walida da Rahama na cikin yara mafi kankantar shekaru- daya shekararta biyu daya kuma uku. Daga baya suma an sake su tare da wasu 'yan yara da ba sa iya ko tafiya sosai. Amma sauran yayyensu uku suna can a hannun 'yan bindiga.

Babbar ita ce Umma 'yar shekara 13 tana kuma son kallan fina-finan yara kamar Tom and Jerry tare da kannenta biyu maza da mata biyu. Har yanzu mahaifiyarsu da ke cike da damuwa ba ta ji labarinsu ba daga wajen masu garkuwa da mutane.

Ranar Lahadin da aka sace yaran, ta ce ta yi maza ta hanzarta zuwa makarantar bayan jin karar bindigar da aka rika harbawa. Abin da ya tilasta mata buya a wani wuri bayan ta ga gwamman masu dauke da makamai sun shiga makarantar.

"Sun karya kwaɗon kofar tare da yi wa yaran ihun su cire takalmansu, domin hana su guduwa. Nan da nan yaran suka fara kuka suna kiran iyayensu.

"Ina ganin ɗana dan shekara biyu na kuka kusa da wani mutum rike da bindiga. Ya daka wa yaron tsawa, ya ce masa ''yi mana shiru!'' saboda yana kiran sunana. A matsayina na mahaifiyarsa ba zan iya yin komai ba a kai," in ji Hadiza.

Map
1px transparent line

Tashin hankali ya ruɗa sauran yaran biyu. Saboda a cewar mahaifiyarsu cikin dare sai su tashi firgice suna ihu, suna ganin kamar za a ƙara zuwa a ɗauke su. Kullum sai sun tambayi, ina yayarsu da dan uwanta suke, yaya gadonsu babu kowa.

Hadiza na koyar da kimiyya ne a wata makaranta da ke kusa da su, amma yanzu an rufe makarantar saboda rashin tsaron da ke damun yankin. Masu garkuwa da mutanen suna neman a biya su kudi da suka kai dalar Amurka 100,000 kafin su saki yaran.

Iyayen yara da yawa daga ciki suna ta fafutukar haɗa wadannan kuɗi. Amma albashin malamin makaranta a yankin bai kai dalar Amurka 400 ba a shekara kwatankwacin naira 200.000, wanda ko kusa da abin da aka nema su biya bai yi ba.

Tana ta fargabar cewa za a manta da 'ya'yanta saboda su ba su da kuɗi.

"Mutane sun manta da su saboda ba 'ya'yan kowa ba ne su. Da a ce 'ya'yan wasu ne, da ba za a barsu a dawa ba na tsawon wadannan makonnin ba tare da jin ɗuriyarsu ba. Haka ba zai taba faruwa ba," in ji Mahaifiyarsu.

Short presentational grey line

'Abu ne mai mahimmanci da sun samu iliminsu'

A ranar 17 ga watan Yuni sama da ɗalibai 80 aka sace daga makaranatar kwana ta Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yawuri a jihar Kebbi.

Mustapha ɗan shekara 14 dan Aminu Umar ne, yana da kanne biyar, kuma gidansu na da nisan kilomita 200 daga makarantarsu, amma saboda muhimmancin ilimi mahaifinsa ya kai shi wannan makaranta domin gina gobensa.

Aminu Umar
Bayanan hoto, Aminu Umar ya dage kan cewa ba zai cire sauran 'ya'yansa ba daga makarantar

Mako guda kafin a sace yaran, wani mahaifi ya cire dansa daga makarantar saboda jin labarin yadda 'yan bingida ke ayyukansu a yankin.

Ya yi kokarin nusantar da Malam Aminu ya cire Mustapha daga makarantar shi ma, amma yana son dansa ya yi jarrabawarsa a makarantar, kuma wasu daga cikin malaman sun ba shi tabbacin cewa yaran za su kasance cikin tsaro da koshin lafiya.

"Na amince da su kan dana. Amma yanzu ba na iya barcin arziki tun da bayan dauke su, kullum tunanina a wane irin hali yanzu 'ya'yanmu suke, a yaya suke barci, shin suna samun ruwa mai tsafta da isasshen abinci," in ji Aminu.

Ya kara da cewa babu wani abin kamawa daga bayanan makarantar, ko kuma gwamnati tun bayan sace yaran kuma yanzu suna cikin fargaba ta kada a cutar masa da dansa.

Amma, matarsa tana ta rokonsa ya cire yan uwan Mustapha daga makarantar amma ya ki sauraron wannan kokenta yana cewa yafi son yaransa su ci gab da karatunsu a inda suke.

"mutane na ta cire yaransu daga makaranta a jihar. Amma dama an barmu a baya ta fannin ilimi, hakan zai iya haifar da matsala a rayuwar yaranmu ta gaba," in ji Aminu.

Short presentational grey line

'In babu tsaro babu maganar ilimi'

A ranar 5 ga watan Yuli, an sace dalibai 120 daga makarantar Bapthel Baptist da ke Kujama a Jihar Kaduna.

Nathan Joseph Kopzuma yaro ne dan shekara 14 na son zama injiniya. Yana son koyar abubuwa kimiyya a makarnta.

Tun daga randa aka sace shi mahaifinsa da ke malamin coci ya ce bai ji duriyarsa ba. Labarin kawai da ake samu shi ne daga makaranta, wadanda suke magana da masu garkuwa da mutanen.

Nathan Joseph Kopzuma

Asalin hoton, Joseph Kopzuma Hirdima

Bayanan hoto, Nathan Joseph Kopzuma na da burin zama injiniya

"A matsayin iyaye mun shiga damuwa. Muna son muyi wani abu damin shiga Tsakani, Amma babu wani taimako. Ba zamu iya ja da su ba, ba zamu iya zuwa inda suke ba, ba mu san inda yaranmu suke ba. Muna cikin damuwa da bakin ciki.

Rabaran Joseph Kopzuma Hirdima ya ce ya yi ta rokon gwamnati su taimaka musu su ceci yaransu a dawo da su gida. Amma daga karshe ya gano basu da wani zabi sai dai yi roki Allah ya shiga lamarin.

An dauki Josep mai shekara wanda da ne a wajen Rebecca Bulus daga wannan makarantar shi ma, ta bayyana kaduwar da ta yi bayan jin labarin an sace danta: " Lokacin da naji labarin duniyar ce ta juyen sama zuwa kasa. Na kusa faduwa, ban taba yin hawaye kamar haka ba, ba zan iya bayyana halin bakin cikin da nake ciki ba."

Tun lokacin da aka sace yaran abu daya take fata, Allah ya sa yaran na nan a raye.

Joseph Bulus

Asalin hoton, Bulus family

Bayanan hoto, Tun bayan sace Joseph Bulus kaninsa ya shiga cikin wani irin tashin hankali

Ta bayyana Joseph a matsayin mai barkwanci, yaro mai son kida wanda yake waka da kuma dukan ganga a coci wani lokacin har da fiyano. Shi ne na biyu cikin yaranta hudu, Duk da cewa yana makarantar kwana amma ya shaku da kansa dake gida yana yawan kiransa su yi magana.

Rabecca ta ce karamin danta har yanzu yana firaimare, kuma kullum cikin tambaya suke kan cewa menene ya faru ga dan uwansu.

Masu garkuwa da mutanen sun nemi kudi mai yawa daga iyayen domin fansar yaransu. Iyalan suna ta kokarin hada kudin, amma fa suna da matukar yawa.

Bulus family

Asalin hoton, Rev Usman

Bayanan hoto, Iyayen Joseph na kokarin yadda za su tattara wadannan kudin fansa

"Muna bukatar tsaro, idan babu tsaro ai babu maganar ilimi. Babban dana yana makarantar kwana shima kullum cikin damuwa nake kan halin da yake. Mun fara tunanin cire shi daga makarantar ma. Muna son zaman lafiya ya samu a kasarmu tukun -daga baya a yi batun neman ilimin," in ji Rabecca.

Bayanan bidiyo, Nigeria child abduction: Kidnappers demand millions for a child's life