Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ashraf Ghani: Taliban ta bukaci shugaban Afghanistan ya sauka daga mulki
Kungiyar Taliban ta ce ba za a samu zaman lafiya a Afghanistan ba sai shugaban kasar Ashraf Ghani ya sauka daga mulki sannan a samar da sabuwar gwamnati.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, mai magana da yawun Taliban, Suhail Shaheen, ya bayyana matsayar kungiyarsu kan makomar Afghanistan.
Ya kara da cewa kungiyarsu ba ta da niyyar yin babakere a gwamnatin Afghanistan.
Hakan na faruwa ne a yayin da gwamnatin Afghanistan ta sanya dokar hana fita a kusan dukkan kasar ranar Asabar a yunkurin hana kungiyar Taliban mamaye birane.
An hana zirga-zirga a dukkan biranen kasar daga karfe goma na dare zuwa karfe hudu na asubahi, idan ban da a Kabul da wasu larduna biyu
Suhail Shaheen na daga cikin wakilan da suka halarci zaman tattaunawar sulhu tsakanin kungiyar Taliban da gwamnatin kasa da aka yi a kasashe daban-daban.
Bayan janyewar sojojin Amurka da na kawancen kungiyar NATO daga Afghanistan, Taliban ta ci gaba da iko da wasu sassan kasar.
A makon da ya wuce, wani babba a rundunar sojin Amurka Janaral Mark Milley, ya shaida wa manema labarai cewa Taliban na ci gaba da mamaya.
Janar Milley bai musanta hasashen da ake yi cewa mai yiwuwa nan gaba kadan Taliban ta karbe iko da daukacin Afghanistan ba.
Suhail Shaheen ya shaidawa AFP cewa, "Bayan tattaunawar da ake yi, za a kafa sabuwar gwamnati a Kabul, wadda dukkan jam'iyyun siyasa za su amince da ita, kuma dole a kawo karshen gwamnatin Ashraf Ghani, daga nan ne kungiyar Taliban za ta ajiye makamanta."
Ya kara da cewa: "Ina son bayyana muku ba mu da niyyar yin babakere a gwamnati, saboda gwamnatocin baya da suka yi kokarin mamaye madafun iko ba su yi nasara ba."
Sai dai Taliban ta kara bayani karara kan abu guda - babu batun sasantawa tsakaninsu da Shugaba Ashraf Ghani.
Suhail Shaheen ya kuma ce Mista Ghani ya rasa damar da yake da ita ta mulkin kasar. Baya ga haka, Taliban na zargin shi da yin magudi lokacin zaben shekarar 2019.
Bayan kammala zaben ne, Ashraf Ghani da abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah suka yi ikirarin yin nasara.
Har wa yau, an cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu inda aka bai wa Mista Abdullah mukami na biyu a gwamnati, sannan aka nada shi mukamin shugaban kwamitin sasantawa na kasa baki daya.
A bangare guda kuma sakatariyar yada labaran fadar White House Jen Psaki, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Shugaba Joe Biden na goyon bayan shugaban Afghanistan.
Shekaru 20 da suka gabata, a lokacin da Taliban ke iko a kasar, an haramta wa 'ya'ya mata zuwa makaranta, ana kuma tilasta wa mutane bin tsarin shari'ar musulunci.
Da dama daga cikin 'yan kasar na fargabar kada a koma 'yar gidan jiya. Yawancin 'yan kasar masu kudi a hannu na ta kokarin samun biza domin ficewa daga Afghanistan.
Kashi 95 cikin 100 na sojojin Amurka da na kungiyar kawancen NATO sun fice daga kasar, yayin da ake da jiran ficewar sauran kashi 5 a ranar 31 ga watan Agusta mai zuwa.