Afghanistan: Dole dakarun Amurka su bar ƙasarmu kamar yadda aka tsara - Taliban

Duk wani sojan ƙasashen waje da ya rage a Afghanistan bayan wa'adin janyewar Nato daga watan Satumba zai kasance cikin hatsari a matsayin mai mamaya, kamar yadda ƙungiyar Taliban ta shaida wa BBC.

Wannan na zuwa ne bayan rahotannin cewa dakaru 1,000 yawancinsu na Amurka za su ci gaba da zama domin kare ofisoshin jakadanci da kuma filin jirgin sama na Kabul.

Wa'adin aikin sojin Nato na shekara 20 a Afghanistan ya ƙare.

Amma rikici a ƙasar na ci gaba da ƙaruwa, inda Taliban ke ci gaba da ƙwace yankuna.

Ƙarƙashin yarjejeniyar da aka yi da Taliban, Amurka da sauran amininanta na Nato sun amince su janye dukkanin dakarunsu da nufin Taliban ba za ta bari al-Qaeda da sauran ƙungiyoyi su yi aiki a yankunan da take iko da su ba.

Shugaba Joe Biden ya tsayar wa'adin 11 ga Satumba - shekara 20 da aka kai harin 9/11 a Amurka - a matsayin lokacin da dakarun Amurka za su fice gaba ɗaya, amma rahotaanni sun ce za a kammala ficewar cikin kwanaki.

Yayin da sojojin Afghanistan ke shirin karɓar ragamar tafiyar da tsaro, fargaba na ƙaruwa a Kabul.

Kakakin Taliban Suhail Shaheen ya ce ƙwace ikon Kabul ba "tsarin Taliban ba ne."

Amma a hirarsa da BBC daga ofishin Taliban a Qatar, ya ce babu wani sojan ƙasar waje - da suka ƙunshi har da na haya - da za su ci gaba da aiki bayan kammala ficewar.

"Idan har suka bar dakarunsu saɓanin yarjejeniyar Doha da aka amince mataki ne da ya rage ga shugabanninmu," in ji Mista Shaheen.

"Za mu mayar da martani kuma shugabanninmu ne za su yanke shawarar ƙarshe."

Ya jaddada cewa ba za a kai wa jami'an diflomasiyya da ƙungiyoyin agaji da ƴan ƙasashen hari ba, kuma babu buƙatar dakarun da za su ba su kariya.

"Muna adawa da sojojin kasashen waje, ba jami'an diflomasiyya ba da ƙungiyoyi masu zaman kansu da ma'aikata da ke aiki ofisoshin jakadanci - wannan shi ne abin da mutanenmu ke buƙata. Ba za mu kawo musu wata barazana ba," in ji shi.

Mista Shaheen ya bayyana ficewar da aka yi makon da ya gabata daga filin Bagram - ɗaya daga cikin babban sansanin sojin Amurka a Afghanistan - a matsayin muhimmin abu.

Amma Farzana Kochai, ƴar majalisa mace, ta ce ana janyewar ba tare da wani mataki ba.

Mai magana da yawun gwamnatin Afghanistan Razwan Murad ya shaida wa BBC cewa gwamnati a shirye take ta tattauna kuma tsagaita wuta da Taliban ya kamata su tabbatar da cewar a shirye take ga tabbatar da ɗorewar zaman lafiya.

Mista Shaheen ya musanta cewa Taliban na da hannu a rikicin baya-bayan nan.

Ya jaddada cewa yankuna da dama sun faɗa ikon Taliban ne ta hanyar tattaunawa bayan sojoji sun ƙi faɗa.

A ranar Lahadi, Taliban ta sake ƙwace wani yanki na kudancin Kandahar. Mayaƙan sun ce yanzu suna da iko da kusan kashi ɗaya bisa huɗu na ƙasar kusan gundumomi 400.

Kakakin Taliban ya bayyana gwamnati mai ci a matsayin 'marar alƙibla' tare da bayyana ƙasar a matsayin 'Daular Islama' - wata alama da ke nuna tsarin yadda ƙungiyar za ta tafiyar da ƙasar kuma da wahala ta amince da buƙatun gwamnatin Afghanistan game da batun zaɓe.

Mista Shaheen ya ce ba a taɓo batun zaɓe ba a tattaunawar tsakanin Taliban da gwamnatin Afghanistan.

Dakarun Amurka sun ƙwace mulki hannun Taliban a Afghanistan a watan Oktoban 2001.

Ƙungiyar ta kasance mai ba da goyon baya ga Osama Bin Laden da sauran shugabanni da aka alaƙatanta da harin 9/11 da aka kai Amurka 11 ga watan Satumba.

Shugaba Biden ya ce ficewar Amurka abu ne da ya dace yayin da sojojin Amurka suka tabbatar da Afghanistan ba ta kasance maɓuyar masu da'awar jihadi ba na ƙasashen waje domin ƙulla kai hare-hare a ƙasashen yammaci.

Shugaban Afghanistan Asharaf Ghani, a nasa ɓangaren ya jaddada cewa dakarun ƙasarsa suna iya wanzar da tsaro, amma da dama sun yi imanin cewa ficewar dakarun wata babbar barazanar Taliban ce ga ƙasar.

Abin da ya faru shekaru 20 na yaƙin Afghanistan

Daga harin 9/11, zuwa gwabza yaƙi, kuma yanzu dakarun Amurka za su janye baki ɗaya, ga abubuwan da suka faru.

  • A 11 ga watan Satumban 2001 al-Qaeda ƙarƙashin jagorancin Osama Bin Laden a Afghanistan ta kai hari mafi muni da aka taba kai wa a Amurka, kusan mutum 3,000 aka kashe
  • Ranar 7 ga watan Oktoban 2001 ƙawancen da Amurka ke jagoranta ya yi ruwan bama-bamai a sansanonin Taliban da al-Qaeda a Afghanistan. Taliban ya ƙi miƙa Osama Bin Laden
  • A ranar 13 ga Nuwamban 2001 gungun mayaƙa masu adawa da Taliban tare da goyon bayan dakarun ƙawancen da Amurka ke jagoranta suka kori Taliban daga Kabul
  • Ranar 24 ga Nuwamban 2004 aka samar da sabon kundin tsarin mulki a Afghanistan wanda ya kai ga gudanar da zaɓe watan Oktoban 2004
  • A ranar 7 watan Disamba Hamid Karzai ya zama shugaban ƙasa na farko ƙarƙashin sabon tsarin mulkin, inda ya yi wa'adi biyu na shekaru biyar
  • A watan Mayun 2006 dakarun Birtaniya suka shiga lardin Helmand, yankin da Taliban ta fi ƙarfi a kudancin Afghanistan
  • A watan Fabrrairun 2009 shugaban Amurka Barack Obama ya ƙara yawan dakarun Amurka a Afghanistan
  • A ranar 2 ga watan Mayun 2011 aka kashe Osama Bin Laden a wani samame da sojojin Amurka suka kai a Pakistan
  • A ranar 23 ga watan Afrilun 2013 aka samu labarin mutuwar shugaban Taliban Mullah Mohammed Omar
  • A ranar 28 ga Disamba Nato ta kammala yaƙi a Afghanistan, Amurka ta janye dakarunta da dama, saura sun rage suna ba sojojin Afghanistan horo tare da taimaka masu
  • A 2015 Taliban ta sake kai mummunan hari a ginin majalisa a Kabul da kuma birnin Kunduz. A shekarar ne mayakan IS suka fara yaƙi a Afghanistan
  • A ranar 25 ga Janairun 2019 shugaban Afghanistan ya ce an kashe sojojin Afghanistan sama da 45,000 tun hawansa mulki a 2014
  • A Fabrairun 2020 Amurka da ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban a Doha, inda Amurka da Nato suka amince su fice cikin wata 14 idan har mayaƙan suka mutunta yarjeniyar.