China ta ƙaƙaba wa jami'an Amurka takunkumi

Asalin hoton, Reuters
China ta fara kakaba wa wasu tarin daidaikun Amurkawa da hukumomi takunkumi a matsayin wani martani da Amurkar ta sanya wa jami'an Chinar takunkumi a Hong Kong.
Daga cikin Amurkawan da abin ya shafa har da tsohon minista ko sakataren kasuwanci Wilbur Ross.
China ta dauki wannan mataki ne yayin da mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurkar Wendy Sherman za ta ziyarci Sin a karshen makon nan.
Matakin da China ta dauka a shekarar da ta gabata inda ta bullo da dokar tsaro ta kasa a Hong Kong sakamakon zanga-zangar gama-gari da ake ta yi ta neman dumokuradiyya, ita ce sanadin wannan sabani a tsakanin manyan kasashen biyu.

Karkashin dokar hukumomin China sun haramta tare da ayyana duk wani yunkuri na neman ballewa ko aware ko hada kai da wasu hukumomi ko kasa ta waje a matsayin babban laifi, da hukuncinsa mafi tsanani shi ne zaman gidan yari na rai da rai.
A sanadin wannan doka ne Amurka ta zaburo ta sanya wa jami'an China a Hong Kong takunkumi, kan rawar da suka taka ta murkushe masu boren a lokacin.
Haka kuma a lokacin Amurkar ta gargadi 'yan kasuwarta kan hadarin da ta ce yana tattare da tafiyar da harkoki a Hong Kong.
Sai kuma a nata bangaren China, ita ma ta yunkuro a wannan karon inda ma'aikatarta ta harkokin waje ta biyo da martani tana cewa, takunkumin na Amurka ba wani abu ba ne face wata makarkashiya ta neman yin kafar-ungulu ga harkokin kasuwancin Hong Kong, wanda abu ne da ya yi matukar saba dokokin duniya da ka'idojin alakar kasashen duniya.
Bayan ta yi wannan shinfida ne kuma sai Chinar ta ce to ita ma za ta sanya wa wasu Amurkawa bakwai da hukumomi ko kamfanoni da suka hada da tsohon Sakataren Kasuwancin na Amurka Wilbur Ross takunkumi.

Asalin hoton, Reuters
Shi dai Mista Ross, a wancan matsayi nasa a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Donald Trump, ya kara yawan kamfanonin China da ba za su yi kasuwanci da na Amurka ba, ba tare da lasisin yin hakan ba. Kamfanonin Chinar da suka hada da katafaren kamfaninta na fasaha Huawei da ZTE.
Sauran daidaikun Amurkawan da takunkumin ramakon na China ya hau sun hada da darektar kungiyar kare hakkin dan adam ta, Human Rights Watch a China Sophie Richardson, da Carolyn Bartholomew, shugabar hukumar hadin guiwa ta nazarin harkokin kasuwani da tsaro tsakanin Amurka da China.
Sai kuma shugaban cibiyar bunkasa dumokuradiyya ta International Republican Institute da ke Amurkar Adam King.
Sai dai a martaninta game da ramakon na China mai magana da yawun fadar Amurkar Jen Psaki ta gaya wa 'yan jarida cewa matakin na China ba zai sa Amurka ko gezau ba.
Ta kara da cewa martanin na China, misali ne na yadda gwamnatin kasar take hukunta daidaikun 'yan kasa da kamfanoni da kungiyoyin farar hula a matsayin wata hanya ta aikewa da sakon siyasa.

Asalin hoton, Reuters
Masomin wannan rikici dai ya faro ne daga sabuwar dokar ta China ta bullo da ita ne ta yaki takunkumin gwamnatin Trump.
Mu'amulla tsakanin gwamnatin China da ta Amurka ta kara tsami ainun a lokacin Shugaba Trump.
Musamman a kan batun asalin cutar korona ta Covid-19 da hakkin dana dam da kuma tsaron intanet.
A karshen wannan makon ne mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurkar Misis Sherman za ta je China a wani yunkuri na sansata alakar.
Za ta kasance ziyarar wani jami'in Amurka mafi girma a karkashin Shugaba Joe Biden.
Mista Ross ya kasance na baya bayan nan cikin tsoffin jami'an gwamnatin Trump da China ta kakaba wa takunkumi
A watan Janairu ta sanar da sanya wa tsohon Sakataren Harkokin Waje Mike Pompeo da wasu jami'ai 27 na gwamnatin Trump takunkumi.
Abin da gwamnatin Biden ta kira wanda ba zai haifar da wani amfani ba kuma na son zuciya ne kawai.











