Me ya sa dangantakar Amurka da China ta ƙara yin tsami zamanin Trump?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Barbara Plett Usher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC a Ma'aikatar Wajen Amurka
Gwamnatin Shugaba Trump ta kara kaimi a wajen fito-na-fito da kasar China a makon jiya, inda ta umarci a rufe ofishin jakadancin china da ke birnin Houston saboda zargin da ta yi cewa ana amfani da ofishin wajen leken asiri.
Wannan shi ne mataki na baya-baya da gwamnatin ke dauka wacce ta kara dagula dangantakar tattalin arzikin da ke tsakaninsu wacce ta yi matukar tsami a cikin shekaru da dama.
Wakiliyar BBC Barbara Plett Usher ta yi nazari kan batun - da kuma irin sakamakon da zai iya haifarwa - a kan Amurka da China.
Mene ne muhimmacin wannan rikici?
Ba wani sabon abu ba ne idan Amurka ta rufe ofishin jakadancinta sai dai wannan yana cike da abin mamaki mai kama da wasan kwaikwayo, wanda ke da wahalar fahimta. Wannan karamin ofishin jakadanci ne ba babba ba, don haka a ba can ake gudanar da tsare-tsare ba. Sai dai yana taka muhimmiyar rawa wajen cinikayya da dangantaka.
Matakin ya sa gwamnatin China ta yi raddi: ta umarci a rufe ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Chengdu, lamarin da ya kara dagula dangantakar difilomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu.
A iya cewa wannan shi ne tsamanin dangantaka mafi muni tsakanin kasashen biyu a watannin baya-bayan nan, lamarin da ya shafi takaita bayar da izinin shiga kasashen, sabbin dokoki game da tafiye-tafiyen ma'aikatan jakadanci, da kuma korar wakilan kasashen biyu. Bangarorin biyu sun dauki matakin ramuwar gayya, sai dai a wannan karon Amurka ce ta fi daukar matakan yin fito-na-fito.
Yayasuka tsinci kansu a wannan hayaniya?
Manyan jami'an gwamnatin Amurka sun bayyana karamin ofishin jakadancin china da ke Houston a matsayin "daya dag cikin manyan masu laifuka" a fanin tattalin arziki, da leken asiri da suna maus cewa ana amfani da shi wajen zuga-gwaiwa-ta-hau-kaya.
Ba wani abu ba ne idan kasa ta sanya na'urorin leken asirin da ba su da yawa a ofishin jakadancinta sai dai jami'ai a Amurka sun ce abin da ke faruwa a ofishin jakadancin China da ke Texas ya yi matukar wuce gona da iri kuma hakan ne ya sa suka aike da kakkaursan martani don nua cewa ba za su ci gaba da kyale irin wannan karya doka karara ba.
"Kwakwaran matakin" da gwamnatin Amurka a kan China wanda ya hada da katse mata hanzari ya zo ne bayan kalamin da shugaban hukumar leken asirin kasar FBI Christopher Wray ya yi a farkon wata. Ya ce barazanar da china take yi wa Amurka ta karu sosai a cikin shekara goma, yana mai cewa yana fitar da sabon tsari kan dakile leken asirin da China ke yi musu bayan kowacce awa 10.
China ta sha musanta dukkan zarge-zargen d ake yi mata sanna ta bayyana matakin rufe ofishin jakadancin Houston a matsayin "wani babban shafa kashin kaji".

Asalin hoton, Getty Images
Masu suka suna nuna shakku kan matakin da gwamnatin Trump ta dauka na rufe karamin ofishin jakadancin China da ke Houston da kuma lokacin da aka rufe shi. "Akwai lauje cikin nadi," a cewar Danny Russel, wanda ya taba zama babban jami'in ma'aiakatar wajen Amurka a yankin Asia lokacin mulkin Shugaba Barack Obama, yana mai cewa an dauki matakin ne domin kawar da hankulan jama'a game da gazawar Donald Trump kan batutuwa da dama a yayin da yake fuskantar zaben watan Nuwamba.
Shin wannan rikicin na da alaka da zaben shugaban kasa?
A wani bangaren yana da dangataka da zabe, ko da yake a gefe guda kuma za a iya cewa ba shi da ita.
"Yana da dangantaka" da zabe saboda Mr Trump bai dauki matakin caccakar China ba sai a baya bayan nan kuma masu tsare-tsarensa na ganin 'yan kasar suna jin dadin yin hakan. Ya dora ne a kan kalaman da ya rika yi a 2016 na kishin kasa inda ya ce China "ta cuci Amurka".
Sai dai ya kara da dora alhakin barkewar annobar korona kan China a yayin da farin jinsa ke ci gaba da raguwa. Sakon da yake aikewa shi ne, China ce sanadin halin da Amurka ta tsinci kanta a ciki game da cutar korona, ba shi ba.
A gefe guda, za a iya cewa matakin "ba shi da dangantaka" da zabe saboda masu tsattsauran ra'ayi a gwamnatin Trump, irin su Mr Pompeo, sun dade suna yin kira da a dauki tsauraran matakai a kan China inda suka sanya dambar wannan rikici da suke ciki.
Shugaban Amurka ya rika kai komo tsakanin yarda da wannan shawara da kuma bukatarsa ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da da inganta "abokantaka" da shugaban China Xi Jinping.
Rufe karamin ofishin jakadancin Amurka a China ya nuna cewa kasar ta China ce ta fi samun farcen susa a rikicin kawo yanzu, kuma fusatar da mahukunta Amurka suka yi kan kumbiya-kumbiyar China game da tafiyar da annobar korona ya kara rurar wutar rikicin.
Ta yaya hakan zai shafi dangantakar Amurka da China?
Rikicin ya yi matukar kazanta - wannan shi ne rikici mafi tun bayan Shugaba Richard Nixon ya dauki matakin yaukaka dangantaka tsakanin kasashen biyu a 1972. Dukkansu na da laifi a cikin rikicin.
Wutar rikicin ta sosa ruruwa ne lokacin da Shugaba Xi Jinping ya hau mulki a 2013 inda ya rika daukar matakai na kama-karya fiye da magabatansa. Matakin da China ta duka na baya-bayan nan na bullo da sabbin matakan tsaro kan Hong Kong da kuma musgunawar da take yi wa Musulmi 'yan kabilar Uighurs, ya hasala Amurka inda ta kakaba mata jerin takunkumi.
Hakan ya zo daidai da matakin gwamnatin Trump na bai wa Amurkawa muhimmanci a kan kowanne lamari wanda kuma yana cikin bayanin da Mr Pompeo ya yi kan China a makon jiya. A ckin kalaman, wadanda suke dauke da alamomin yakin cacakr baka, ya zargi shugabannin China da kasancewa masu kama-karya da ke son mamaye duniya, sannan ya kwatanta gogayyar da Amurka ke yi da China cewa tamkar 'yanci ne da kuma kama-karya.













