China da Amurka na neman sanya zare kan Musulmin Uighur

Trump

Ma'aikatar wajen kasar China ta yi kakkausan suka ga aniyar shugaba Trump na Amurka ta sanya hannu kan wata doka da za ta bai wa Amurkar damar kakaba wa jami'an kasar China jerin takunkumi.

Dokar dai na hakon kasar ta China ne kan tsare musulmi marasa rinjaye 'yan kabilar Uighur da ke lardin Xinjing na kasar ta China.

Jami'an China sun bayyana yunkurin tamkar wani hari kan tsare-tsare kasarsu, inda kuma suka yi barazanar mayar da martanin da zai sa Amurkar ta gwammace kida da karatu.

Da ma dai tsohon mai bai wa shugaba Trump shawara kan tsaro wadda mista Trump, John Bolton dai ya yi zargin cewa Mista Trump ya shaida wa takawaransa, na China Xi Jinping cewa, ya amince da sansanonin da ake tsare da musulmin 'yan kabilar Uighur.

Ya kara da cewa gina su wani abu ne da ya dace kuma aka yi a kan gaba.

Mista Bolton ya bayyana wannan ne a wani bangare na littafin da zai wallafa a mako mai zuwa kan abin da ya sani dangane da fadar White House.

A ranar Alhamis ne fadar ta White House ta shigar da kara ta neman dakatar da John Bolton daga wallafa littafin a mako mai zuwa.