Hotunan yadda China ke bikin shekara 100 na jam'iyyar kwaminisanci
Shugaban China Xi Jinping ta yi gargadi ga manyan kasashen duniya cewa zai "ladabtar da su" idan suka ɗaga wa kasarsa yatsa ko kuma suka yi yunkurin yi mata matsalandan.
Ya gabatar da jawabi mai zafi a wajen bikin cikar jam'iyyar kwaminisanci ta kasar shekara 100 da kafuwa ranar Alhamis.
Kazalika Mr Xi ya ce kasarsa ba za ta bari "masu shisshigi" su juya ta ba, abin da ake ganin tamkar hannunka-mai-sanda ne ga Amurka.
Ya gudanar da bayanin ne a yayin da China take ci gaba da shan suka game da zarge-zargen take hakkin dan adam da kuma musguna wa Hong Kong.
Dangantaka tsakanin Amurka da China ta yi tsami a shekarun baya bayan nan a kan cinikayya da leken asiri da kuma annoar korona.
Batun Taiwan na cikin abubuwan da ke jawo tayar da jijiyoyin wuya. A yayin da dimokradiyyar Taiwan take kalln kanta a matsayin kasas mai cin gashin kanta, China a kallonta a matsayin wani yankinta da ya balle.
Dokokin Amurka sun ba ta damar taimaka wa Taiwan domin kare kanta idan Chna ta yi amfani da karfi wajne mamaye ta.
A bayanin da Mr Xi ya yi ranar Alhamis, ya jaddada cewa "jimirin" China na sake hadewa da Taiwan.
Ga wasu ƙayatattun hotunan yadda China na bikin cika shakara 100 da kafuwar jam'iyyar kwaminisanci da ke mulkin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar mai suna Chinese Communist Party (wato CCP a turancin Ingilishi), an kafa ta ne a 1921, kuma ta karbe mulki shekara 72 da su ka gabata bayan wani yakin basasa mai tsawo.

Asalin hoton, Getty Images
Jiragen yaƙi na China yayin da su ke wasanni a dandalin Tiananmen ranar 1 ga watan Yuli 2021 a birnin Beijing.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗalibai na daga tutocin China gabanin fara bukukuwan a dandalin Tiananmen a ranar 1 ga watan Yulin 2021.

Asalin hoton, Getty Images
A makonnin da suka gabata China ta baje koli na bikin cika shekara 100 da samar da jam'iyyar kwamimisancin ƙasar

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Tun watan Afrilu aka ba gidajen silman China umarnin nuna wasu fina-finai na farfaganda masu suna "jajayen fina-finai", a kalla sau biyu a kowane mako.
Akwai kuma wata waƙa mai suna "Kashi 100 bisa 100" da aka fitar da ke yaba ci gaban da China ta samu, waƙar da mawakan gambara 100 suka rera ta.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai kuma wani shirin tallata wuraren shakatawa mafi burgewa a cikin China mai suna "Jan yawon buɗe idanu", wanda a karkashinsa aka bayyana wasu wurare 100 na musamman ga masu sha'awa.

Asalin hoton, Getty Images











