Haiti : An bankaɗo wanda ya bada umarnin kisan shugaban ƙasar

Shugaban 'yan sandan kasar Colombia ya ce wani tsohon jami'in ma'aikatar shari'ar Haiti ne ya ba da umarnin kisan shugaban kasar Jovenel Moise.

Shugaban sojojin Cuba Janar Jorge Luis Vargas ya ce da farko Joseph Felix Badio ya fada wa tsoffin sojojin Colombia biyu da ke kula da gungun wasu sojojin haya na Colombia cewa za su kama shugaba Moise, amma 'yan kwanaki kafin hakan sai ya gaya musu cewa shirin ya canja, don haka dole ne su kashe shi.

Mista Badio na daya daga cikin mutane da dama da 'yan sandan Haiti ke nema, inda ake zarginsa da da kisan kai, da shirya kisan da kuma shirya yadda ya faru.

Matashiya

An harbe Mista Moïse ne a makon da ya gabata a wani gidansa na kansa.'Yan sandan Haiti sun ce gungun wasu sojojin haya da suka kunshi tsoffin sojojin Colombia ne suka kashe Mista Moïse.

Shugaban Cuba Ivan Duque ya ce akasarin 'yan kasar ta Colombia da suka shiga wannan aiki an yaudare su ne yayin da aka ce musu za su yi aiki a matsayin masu tsaron lafiyar manyan mutane a Haiti.

Dukkan mutane 28 da ake zargi da kisan tsohon shugaban 'yan Colombia ne, in banda wasu AMurkawa biyu daga cikinsu.

Su wanene suka shirya kisan ?

Tun da farko dai matar marigayi Shugaba Jovenel Moise na Haiti ta zargi makiyansa a siyasa da amfani da sojin haya wajen halaka shi domin a dakile duk wani yunkurinsa na yin garambawul a kundin tsarin mulkin kasar da kuma inganta rayuwar jama'a.

Cikin wani sakon murya da aka wallafa a Twitter, matar marigayin ta yi kira ga al'ummar kasar Haiti da su ci gaba da gwagwarmaya tare da alkawarin mara musu baya.

Martine Moise ta ji rauni lokacin da ƴan bindigar suka yi dirar mikiya a gidan tsohon shugaban yayin da suke kokarin halaka shi.