Yadda wani uba ya hadu da ɗansa da aka yi garkuwa da shi bayan shekara 24

Wani mahaifi ɗan China ya hadu da ɗansa bayan bayan shafe tsawon shekara 24 yana laluben gano shi har ta kai ya niki gari inda ya yi tafiyar sama da kilomita 500,000 kan babur a sassan ƙasar duk don neman ɗan nasa.

Ɗan Guo Gangtang dai ya shiga hannun wasu masu safarar mutane da suka yi gaba da shi a gaban gidansu da ke Lardin Shandong.

Ɓatan ɗan nasa ya ja hankali har aka shirya wani fim a 2015 da a ciki aka haska tauraron ɗan fim a Hong Kong Andy Lau.

Sace-sacen yara babbar matsala ce a China inda ake gaba da yara dubbai kowace shekara.

A cewar ma'aikatar da ke kula da tsaron al'umma, ƴan sanda sun samu nasarar gano ɗan ta hanyar gwajin ƙwayar halitta DNA.

An kuma gano mutanen biyu da ake zargi tare da kama su, kamar yadda jaridar Global Times ta rawaito.

Waɗanda ake zargin waɗanda suke son juna a lokacin da lamarin ya faru, sun tsara yin garkuwa da yaro da nufin sayar da shi domin samun kuɗi, a cewar wani rahoto na China News.

Bayan gano ɗan Mista Guo yana wasa shi kaɗai a ƙofar gidansu, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin da sace shi da aka bayyana da sunan mahaifinta Tang, ta damƙe hannunsa tare da kai shi tasha inda saurayinta mai suna Hu yake jiranta.

Mutanen biyu sun tsallaka zuwa Lardin Henan - wajen da suka sayar da yaron.

Farin ciki mara misaltuwa

Mista Guo da mai ɗakinsa sun zubda hawayen farinciki tare da rungumar ɗan nasu lokacin da suka haɗu da shi Liaocheng, Shandong,ranar Lahadi, a cewar kafar yaɗa labaran CCTV.

"Ɗana, ka dawo!" in ji mahaifiyarsa wadda ba a bayyana sunanta ba cikin wani bidiyo.

Bayan ɓatan ɗansa a 1997, Mista Guo ya je Lardi fiye da 20 da ke sassan ƙasar kan babur ɗinsa duk a ƙoƙarin gano inda ɗansa yake.

Sanadiyyar hakan, ya samu karayar ƙashi lokuta da dama sakamakon haɗarurruka a wasu lokutan kuma, ya yi gamo da ƴn fashi kan titi.

Mahaifin ya zama fitaccen ɗan ƙungiyar mutanen da suka ɓata a China sannan ya taimaka wa wasu iyayen kimanin bakwai sake haɗuwa da yaransu da aka sace.

Sace-sace da safarar jarirai matsala ce da aka shafe shekaru ana fama da ita a China.

A 2015, an ƙiyasta cewa ana sace yara 20,000 kowace shekara a China. Akasarinsu ana sayar da su ga wasu mutanen a ciki da wajen ƙasar.