Alhaji Alhassan Adamu: 'Yan bindiga sun saki Sarkin Kajuru

Bayanai daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa 'yan bindigar da suka sace Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu sun sake shi.

Babban dan Sarkin, wanda kuma shi ne Madakin Kajuru Alhaji Musa Alhassan Adamu, ya tabbatar wa BBC Hausa cewa an saki mahaifin nasu dazun nan.

A cewarsa, suna zaune a gida da rana sai kawai suka ga sarkin ya shigo.

Sai dai ya kara da cewa ba a saki sauran mutum 13 da aka sace tare da sarkin ba.

Alhaji Musa Alhassan ya ce mahaifin nasu yana cikin koshin lafiya kuma ya shiga wanka inda suke jira ya fito sanna su kai shi asibiti domin a duba lafiyarsa.

Ya ce mazauna garin suna ta murna sakamakon sakin sarkinsu.

A wani garejen jawabi da ya yi a fadarsa jim kadan bayan ya fito waje, Alhaji Alhassan Adamu ya ce "jama'ar Kajuru, ina yi muku barka da saduwa da ni", sai kawai ya fashe da kuka.

Da tsakar daren Lahadi ne wasu 'yan bindiga a kan babura suka kai hari kan masarautar Kajuru inda suka sace sarkin, mai shekara 85 tare da mutum 13, ciki har da jariri.

Bayanai sun nuna cewa sarkin ya gudanar da taro ranar Juma'a kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankinsa.Wannan lamari na faruwa ne kasa da mako guda da sace daliban makarantar sakandaren Bethel Baptist fiye da 100 da ke karamar hukumar Chukun a jihar ta Kaduna.

Kazalika harin na zuwa ne mako guda bayan sace wasu mutane, ciki har da jarirai, a asibitin masu larurar kuturta da tashin-fuka da ke Zaria.

Jihar Kaduna na fama da hare-haren 'yan bindiga inda wani rahoto da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar a watan Afrilu ya nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na 2021 an kashe mutum 323 tare da yin garkuwa da mutum 949 a jihar.

Gwamnatin jihar ta Kaduna, karkashin jagorancin Gwamna Nasir Elrufai, ta sha jaddada cewa ba za ta yi sulhu da 'yan bindigar da ke garkuwa da mutane ba, tana mai cewa babban burinta shi ne ta kawar da su.