Irin wahalar da manoman kashu ke sha a Guinea Bissau

Asalin hoton, Ricci Shryock
Kashu ce babbar abinda Guinesa Bissau ke fitarwa zuwa kasashen waje don samun kudin shiga, to amma manoman ƙasar na cin kwakwa kafin su ci moriyar nomanta kamar yadda za a iya gani a cikin wadannan hotuna.

Asalin hoton, Ricci Shryock
Alciony Fernandez ta fito ne daga gidan da a ke noman kashuna, kuma kamar yadda ake iya gani tana shirin ɗaukar ƴaƴanta zuwa kasuwa don ta saida.
A duk kilo ɗaya za ta samu kudin CFA 350 wanda ya yi dai dai da 0.65 na dalar Amurka.

Asalin hoton, Ricci Shryock
Farashin da gwamnati ta saka wa kayan gona a Guinea Bissau ya fado da kashi daya bisa uku tun shekarar da ta wuce, kuma akan ya faru ne saboda zuwan annobar Korona.
Bugu da ƙari tun farkon shekarar nan manoman kashuna a Guinea Bissau ke fama da harajin da gwamnati ta ƙaƙaba na CFA 15 ga duk kilo daya na kashuna.
Hakan ya sa masu fitar da kayan gonar suka fara tunanin canza shawara game da sayenta saboda ƙarin kudin da ake musu.

Asalin hoton, Ricci Shryock
Amma a watan da ya gabata an samu sauƙi, bayan da gwamnati ta cire tara ga manoma, ta kuma rage haraji kan kayan gona da manoma ke fitarwa.
Guinea Bissau ta saba fitar da kashuna ton 200,000 a duk shekara, to amma a bara ya sauko zuwa 160,000.
Sai dai kuma wan labari marar daɗin ji shi ne Indiya da ta fi kowace ƙasa sayen kashuna daga Guinea Bissau na fama da annobar Korona, a cewar Mamadou Yerro Djamanca na kungiyar masu fitar da kashuna daga Guinea Bissau.
Ya kara da cewa kayan gonar na nan jibge a ƙauyuka manoma na jiran a zo a saye a fita da shi.

Asalin hoton, Ricci Shryock

Da zarar damina ta shigo musamman wuraren ƙarshen watan Mayu zuwa tsakiyar Yuni, abu ne mai wahala a iya dakon kashuna zuwa wasu bangaroran ƙasar saboda ambaliya da kuma taɓo.

Asalin hoton, Ricci Shryock
Neia Nianta ta mallaki hekta 1.5 da ta ke noma kashuna a ciki, kuma tana girbi a tsakanin watannin Maris zuwa Yunin kowace shekara.
Ta kan shafe wuni tana aikin girbin.
Giyar kashuna wadda ake samarwa ta hanyar ruwanta ta yi suna a Guinea Bissau.

Asalin hoton, Ricci Shryock
A nan Neia na aiki tare da Quinta Cabi. Sun ce suna samun cinikin kamar CFA 5,000 a rana na basarar kashuna.
A cewar Neia ''bara mun fi samun riba. Mun fi sayar da barasa mai yawa kuma da tsada.''
Ta kara da cewa '' annobar Korona ce ta kawo mana cikas bana.''
''Aikin matsar kashuna yana da matukar wahala. Na farko muna katso wa daga bishiyarta, daga nan kuma mu raba ta daga ƙodagonta, sannan mu fara matsarta.'' inji Neia.
A cewarta sukan cika bokiti huɗu ko biyar, wanda ke samar musu da lita 25 ta barasar.

Asalin hoton, Ricci Shryock
Amma kuma akwai abun sha da ake yi da ba shi da haɗi da giya, a cewar Kumus da Silva.
''Muna anfani da inji na gargajiya don matsa kashuna mu haɗa abun sha.'' inji Da Silva.

Asalin hoton, Ricci Shryock
Ya kuma ce suna cire ƙodagon kafin su matse ta.

Asalin hoton, Ricci Shryock
A shekarar farko da ya hada abun sha na kashuna don sayarwa bai samu riba ba.
To amma yanzu yana samun CFA 500 a duk kwalba ɗaya idan ya sayar da ita ga gidajen abinci.
''Abin da ke bamu matsala shi ne rashin tallata hajarmu, saboda mutane ba sa nemanta don su saya idan ba mu muka tallata ta ba.''
''Saboda haka idan muka tallata musu ita da kansu za su riƙa nemanta''. in ji Da Silva.
Duk da kashuna ta zama kayan gona da ya samu karɓuwa a Guinea Bissau, har yanzu akwai babbar barazana da ke tunkaro masu nomanta da kuma raba ta, lura da yadda lamurra ke tafiya a halin yanzu.

Asalin hoton, Ricci Shryock











