Ramadan: Hotunan yadda masu aikin ƙarfi ke neman abinci a lokacin azumi

A mafi yawan lokuta ana gudanar da azumin watan Ramadan ne a Najeriya a lokacin zafi.

A wannan shekarar ma 'yan Najeriya, musamman wadanda ke zaune a arewacin kasar, suna fama da zafi a lokacin azumi.

Hakan ya sa a lokuta da dama za ka ga masu aikin ƙarfi na neman abinci cikin zafin rana.

Yayin da ake shirin shiga kwanaki goma na ƙarshe na watan Ramadan, mun kawo muku jerin hotunan yadda al'ummar musulmi a Najeriya da ke aikin ƙarfi ke neman abinci da azuminsu a baki.

Anan wani dattijo ke tura kurar ruwa yana neman masu saye wataƙila don suyi aikin abincin buɗe baki
Bayanan hoto, Anan wani mutum ne yake tura kurar ruwa yana neman masu saye wataƙila don su yi aikin abincin buɗe baki a birnin Kano...
Anan ma wani dattijo ne ke zagayawa yana sayar da kaya a kan titi duk da rana da ake tsalawa
Bayanan hoto, A nan ma wani dattijo ne ke zagayawa yana sayar da kaya a kan titi duk da rana da ake tsalawa
Wani mai sana'ar faskare ke nan a bakin aiki da azuminsa a baki
Bayanan hoto, Wani mai sana'ar faskare ke nan a bakin aiki da azuminsa a baki
Wasu matasa ke yanka katako kafin buɗe baki
Bayanan hoto, Wasu matasa ke yanka katako kafin buɗe baki
Wani yaro da ke sana'ar jari-bola da tsakiyar rana.
Bayanan hoto, Wani yaro da ke sana'ar jari-bola da tsakiyar rana.
Matsashi na aikinsa na Kafinta da tsakar rana
Bayanan hoto, Matsashi na aikinsa na kafinta da tsakar rana
Wadannan masu sana'ar sayar da ruwan baron suna tallan ruwan da tsakar rana
Bayanan hoto, Wadannan masu sana'ar sayar da ruwan baron suna tallan ruwan da tsakar rana
Wani mai sana'ar wanki da guga kenan a bakin aiki da tarin kaya a gabansa
Bayanan hoto, Wani mai sana'ar wanki da guga ke nan a bakin aiki da tarin kaya a gabansa