Ramadan: Hotunan yadda masu aikin ƙarfi ke neman abinci a lokacin azumi

A mafi yawan lokuta ana gudanar da azumin watan Ramadan ne a Najeriya a lokacin zafi.

A wannan shekarar ma 'yan Najeriya, musamman wadanda ke zaune a arewacin kasar, suna fama da zafi a lokacin azumi.

Hakan ya sa a lokuta da dama za ka ga masu aikin ƙarfi na neman abinci cikin zafin rana.

Yayin da ake shirin shiga kwanaki goma na ƙarshe na watan Ramadan, mun kawo muku jerin hotunan yadda al'ummar musulmi a Najeriya da ke aikin ƙarfi ke neman abinci da azuminsu a baki.