Earth Day 2021: Matakai 10 da za ku bi domin ceto duniya daga gurɓacewa

Landscape

A ranar Alhamis ne ake bikin Ranar Alkinta Muhalli ta Duniya wadda ake gudanarwa ranar 22 ga watan Afrilun kowacce domin jan hankulan jama'a su lura da muhallansu.

Taken wannan shekara shi ne "Dawo Da Martabar Duniyarmu" wato "Restore Our World" a turance, kuma ana gudanar da taruka a fadin duniya domin koya wa mutane bukatar dawo da martabar muhallansu.

Ayyukan da dan adam ya kwashe shekara da shekaru yana yi a doron kasa sun yi matukar gurbata muhalli lamarin da ya ta'azzara sauyin yanayi da haifar da cutuka.

Masana na ganin rashin alkinta muhalli shi yake haifar da tsananin zafin da ake fama da shi a wasu kasashe da yankunan duniya, ciki har da arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar da ma Kamaru.

Najeriya na fama da matsalolin da suka shafi muhalli wadanda suka hada da gurgusowar hamada da zaizayar kasa da ambaliyar ruwa da makamantansu.

Masu rajin kare muhalli sun zayyana wasu hanyoyi da suke ganin sun kamata a bi domin inganta muhallai.

Earth Day: Wetin you fit do to 'Restore Our World'

Asalin hoton, Other

Ga wasu daga cikin hanyoyin da za ku bo domin alkinta muhalli:

  • Rage zubar da shara a ko ina.
  • Ka rika share wurin da kake zaune domin radin kanka
  • Ka koya wa wasu yadda za su alkinta muhalli
  • Yi kokarin rage yawan ruwan da kake barnatarwa
  • Kada ka sayi kayan da za su yi illa ga muhalli
  • Ku rika sayen abubuwan da za su dade kuna amfani da su
  • Ku yi amfani da kwan lantarkin da ba shi haske sosai domin rage gurbatacciyar iska
  • Ku dasa bishiyoyi
  • Idan ya zama wajibi ku yi amfani da sinadari domin wanke-wanke da gyaran gida, ku sayi wanda ba shi da illa sosai
  • Ba kodayaushe ne ya kamata ka tuka mota ko babur ba, idan da hali ku rika hawa keke domin rage hayakin da ke dumama duniya