Bidiyo: Google ya gano yadda duniya take sauyawa

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Google ya gano yadda duniya take sauyawa

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Google Earth ya kaddamar da wata taswira mai nuna yadda doron duniya ke sauyawa da gushewar zamani.

Tana amfani da hotunan da aka dauko da tauraron dan adam shekaru 37 da suka gabata zuwa yanzu.

Tana taimakawa wajen nuna tasirin sauyin yanayi muraran.

Haka kuma ta nuna yadda ayyukan dan adam suka sauya doron duniya.